Ƙaramar Ministar Abuja, Dr. Mariya Bunkure ta Faranta Zukatan Tsofaffin Abokan Aikinta Na AKTH
Daga Sunusi K/Naisa
Read also: Mazauna Kusa Da Madatsar Ruwa ta Ghari Da Su Yi Nesa Da Kogi – Inji Shugaban Ƙaramar Hukuma
Ƙaramar Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Dr. Mariya Mahmoud Bunkure ta sauke Kaɓakin arziƙi ga tsofaffin abokan aikinta na Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH).
Babban Mataimaki na musamman ga Ƙaramar Minista, kan kafofin sada zumunta na zamani, Bin Usman Rano ya sanarwar da jaridar The Stentor news-Hausa.
Kaɓakin arziƙin da Ministan ta rabawa ma’aikatan sun haɗar da miliyan ɗaya-ɗaya (₦1,000,000), a inda wasu aka basu Naira dubu dari biyar(₦500,000), wasu kuma Naira dubu dari biyu da hamsin (₦250,000), wasu dubu dari, wasu kuma Naira dubu hamsin (₦50,000) kowannensu.

Babbar Kotun Tarayya Abuja ta yanke hukunci ga wanda ya kitsa munanan hare-hare a Kano
Read also: Rashin Kulawa Na Daga Cikin Bukatun Da Matar Gwamna Abba Ta Kai Kara A Kotu Don A Raba Su
Da yake jawabi yayin bada kaɓakin arziƙin, Dr. Idris Ado Muhammad (Adebo), wanda shi ya wakilci Ƙaramar Ministar Abujan wajen miƙa saƙon tallafin, ya ce wannan abin alkhairi yana nuna kyakkyawar dangantaka da aka samu a lokacin Minista tana a matsayin ma’aikaciya lafiya a asibitin tare da alƙawarin ci gaba da zuminci mai ɗorewa.
” Yana daga cikin ƙudure-ƙuduren Minista na cigaba da tallafawa ma’aikatan da ke tare da ita da sauran al’umma a duk lokacin da ta samu damar”.
Ya ƙara da cewa batun cigaba da tallafawa abokan aikin nata na Asibitin yanzu ne aka fara, za’a cigaba da yi lokaci zuwa lokaci dan tallafawa sauran ma’aikatan.

Da yake jawabi, Shugaban Asibitin Koyarwar Malam Aminu Kano (AKTH) CMD, Prof. Abdurrahman Abba Sheshe, ya ce abubuwan da take musu ba za su ƙidayu ba, sai dai su roƙi Allah Ya saka mata da mafi girman alkhairi ya kuma ƙara ɗaukaka matsayinta.
Farfesa Shehe ya ce cikin ma’aikatan da sukai aiki tare, bayan waɗanda ta basu kaɓaken alkhairi irin wannan, akwai masu yawa da ta biyawa kujerar aikin hajji, ya ce ko a shekarar 2024 da ya je Makka ya ga ma’aikatan sa da dama da ita ta biya musu. Har ma da marasa lafiyar da ita ce kan duba su a da taimakonta kan isa gareshi har yanzu. Haka kuma a halin yanzu ta saka kuɗi domin a faɗaɗa sashen Family Medicine na AKTH. Saboda haka ake cewa ‘naka sai naka’. Muna fatan Allah ya cigaba da yi mata jagora.
Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mata Biyar A Shanono
Da yawa daga cikin waɗanda suka ci gajiyar taimakon Ministar sun gode mata da kuma fatan ta gama lafiya.



























