Daraktoci 6 Na Ma’aikatar Tsaro Ta Kasa Sun Faɗa Komar Yan Bindiga
Daga Wakilinmu
Fargaba ta mamaye ma’aikatan gwamnatin tarayya bayan da yan bindiga suka sace daraktoci shida na Ma’aikatar Tsaron Ƙasa a kan hanyar Kabba zuwa Lokoja.
Read also: Shugaban ‘Yan Bindiga Bello Turji Na yunƙurin Miƙa Wuya Bayan Mutuwar Yelo Danbokolo
Rahotanni sun ce an sace su ne a ranar Litinin, 10 ga Nuwamba, 2025, yayin da manyan jami’an ke tafiya daga Legas zuwa Abuja domin jarabawar karin girma.
Majiyoyi sun shaida wa Jaridar vanguard cewa maharan sun yi kwanton-bauna tare da tare ayarin motocin jami’an, inda suka yi awon gaba da su zuwa wani wuri da har yanzu ba a gano ba.
Read also: Jami’an Tsaro Sun Yi Arangama Da Al’ummar Gari A Garko Har An Kone Motar ‘Yan Sanda
Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mata Biyar A Shanono
Read also: Sama da ‘Yan Bindiga 150 Sun Nutse a Kogin Sokoto
Kungiyar Association of Senior Civil Servants of Nigeria (ASCSN) a wata sanarwa da shugabanta, Shehu Mohammed, da Sakatare Janar Joshua Apebo suka fitar, ta bayyana sunayen daraktocin da aka sace kamar haka:
Mrs Ngozi Ibeziakor da Mrs C.A. Emeribe da Mrs C. Helen Ezeakor da Mrs C.A. Ladoye da Mrs J.A. Onwuzurike da kuma Mrs Catherine O. Essien.
Sanarwar ta kara da cewa, dukkansu ma’aikatan Command Day Secondary School (CDSS) Ojo, Lagos ne, kuma mambobin kungiyar kwadago.
Sanata Barau, Rashin Dattakon Alwan da Afkawar Ramin Ramat
Harin ya sake nuna karuwar matsalar garkuwa da mutane a kan manyan titunan Najeriya, lamarin da ke ci gaba da zama barazana ga jami’an gwamnati da sauran matafiya. (Inda Ranka).




























