Hukumar KAROTA Zata Samar Da Motocin Sufuri Ga Ɗaliban Jami’ar Sule Lamido Dake Jigawa
Daga Sunusi K/Naisa
Read also: An Yi Kira ga Karamar Hukumar Sumaila da ta Samar da Bandaki a Makarantar Liman Yau JASS Sumaila
Hukamar kula da zirga zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, ta bayyana shirinta na samar da motocin zirga zirga ga daliban Jami’ar Sule Lamido ta kafin Hausa da ke jihar jigawa, yan asalin Jihar Kano, domin saukake musu harkokin sufuri daga Kano zuwa Jihar ta Jigawa.
Ga Wani Labarin:Sarakunan Jama’are Da Ningi Na Miƙa Ta’aziya Bisa Rasuwar Durbin Kano
Shukagaban hukumar ta Karota Injiniya Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana hakan yayin da ya karbi bakuncin kungiyar daliban Jami’ar ta Sule Lamido kafin Hausa a makon da muke ciki.
Ta cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na hukumar Abubakar Ibrahim Sharada ya fitar a yau Asabar 1 ga watan Nuwamba 2025, shugaban hukumar Karota ya kuma bukaci daliban da su kasance jakadu na gari da Jihar Kano za ta yi al’fahari da su a nan gaba.
Shugaban hukumar ya kuma yi al’kawarin sanya hannu wajen samar da dakunan kwana ga daliban na jihar Kano su sama da Dubu Hudu, a wani mataki na rage musu kudaden da suke kashewa na dakunan kwanan dalibai, baya ga tallafin karatu.
Injiniya Faisal Mahmud Kabir, ya godewa wadannan dalibai bisa ziyara da suka kawo masa. Tare da bayar da tabbacin cigaba da tallafa musu a duk lokacin da bukatar hakan ta taso
Read also: Karamar Hukumar Ghari Ta Raba Takardun Daukar Aiki Ga Malamai 50
Ga Wani Labarin:Shugaban Hukumar KAROTA Ya Karɓi Baƙuncin Shugabannin Hukumar Kashe Gobara Ta Tarayya, Reshen Kano.
Da ya ke nasa jawabin shugaban kungiyar daliban Jami’ar Sule Lamido ta Kafin Hausa Comrade Habibu Abdullahi Abubakar ya ce sun kai wannan ziyara ne ofishin hukumar KAROTA domin mika bukatun su, da kuma kara kulla alaka tsakanin kungiyar daliban da kuma hukumar Karota.




























