Connect with us

Hi, what are you looking for?

Tsaro

Jita-Jitar Juyin Mulki Ba Gaskiya Bane Kuma Makirci Ne — Shelkwatar Tsaro

Shelkwatar Tsaro (HDQ)
Shelkwatar Tsaro (HDQ)

Jita-Jitar Juyin Mulki Ba Gaskiya Bane Kuma Makirci Ne — Shelkwatar Tsaro
By Sunusi K/Na’isa

Shelkwatar Tsaron Najeriya ta ƙaryata rahoto da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke zargin cewa an yi yunƙurin juyin mulki don hambarar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tana bayyana rahoton a matsayin ƙarya da makirci, kuma zai iya haifar da tashin hankali da kawo firgici a ƙasa.

Sanarwar da aka wallafa a shafin X na hukumar tsaron ta ƙasa, wacce Daraktan Bayar da Bayanai na Tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya sanya wa hannu, hukumar ta roƙi ‘yan Najeriya da su yi watsi da abin da ta kira “ƙarya da makiyan ƙasa ke yadawa.”

“Dakarun Sojojin Najeriya suna nan daram cikin biyayya ga Kundin Tsarin Mulki da Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa kuma Babban Kwamandan Sojoji, Alhaji Bola Ahmed Tinubu, GCFR,” in ji sanarwar.

Martanin rundunar ya biyo bayan wani rahoto da Sahara Reporters ta wallafa, inda ta danganta soke bikin zagayowar cikar Najeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai da wani zargin yunƙurin juyin mulki.

Ga Wani Labarin:Gwamnatin Kano Na Faɗakar Wa Kan Cutar Lassa, Ta Ja Hankali Game Da Haɗarin Yaɗuwar Cutar

Wannan jarida ta kuma danganta lamarin da wata sanarwar da Shalkwatan Tsaron (DHQ), ta fitar a baya, inda ta bayyana cewa an kama sojoji goma sha shida (16) da ake bincike a kansu bisa wasu zarge-zargen karya ƙa’idojin aiki — abin da jaridar ta danganta da zargin yunƙurin juyin mulkin.

Sai dai DHQ ta bayyana cewa wannan bincike na cikin tsarin horo da gyaran hali na cikin gida ne da ake gudanarwa a kai a kai domin tabbatar da ƙwarewa da mutunci a cikin rundunar soji.

“An kafa kwamitin bincike bisa ƙa’ida, kuma sakamakon binciken zai kasance a fili nan gaba,” in ji sanarwar.

A cewar DHQ, dalilin soke bikin cikar Najeriya shekara 65 ba shi da nasaba da wani yunƙurin juyin mulki, illa kawai dalilin gudanar da wasu muhimman tattaunawar diflomasiyya da Shugaban Ƙasa ya halarta a ƙasashen waje, tare da baiwa sojoji damar mayar da hankali kan yaƙi da ta’addanci da ‘yan ta’adda, da ‘yan bindiga a faɗin ƙasar Najeriya.

Ga Wani Labarin:BARAYI SUN GUNTULE HANNUN MATASHI A JIHAR KEBBI

A halin yanzu, majiya daga cikin rundunar soji ta tabbatar da cewa an kafa wani kwamiti na bincike na cikin gida wanda ya ƙunshi wakilai daga Rundunar Sojin ruwa da, Sojin Sama da ‘Yan Sanda da Hukumar Tsaro ta DSS domin nazarin laifukan da suka shafi rashin ladabi da karya doka a tsakanin waɗanda ake zargi.

Shelkwatar Tsaro ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da kare tsarin mulki da tabbatar da ƙwarewa da mutunci a aiki, da kuma kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar, tare da gargaɗin masu ƙoƙarin haifar da rikici tsakanin sojoji da al’umma.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...