MAJALISAR DOKOKIN JIHAR BAUCHI TA SAURARI RA’AYOYIN JAMA’A GAME DA KIRKIRO SABBIN MASARAUTU
Daga Muazu Hardawa, Bauchi
Read also: Murtala Garo Zai Bayyana A Majalisar Dokokin Kano Don Tantancewa
Majalisar dokokin jihar Bauchi ta shirya zama don jin bahasi daga Jama’ar jihar Bauchi game da shirin kirkiro masarautu da hakimai da gundumomi a jihar Bauchi.
Zaman wanda ya gudana a Hazibal Hotel da ke hanyar Dass ya kasançe a karkashin jagorancin kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi Hon. Alhaji Abubakar Y. Sulaiman tare da goya bayan ‘yan majalisar sama daguda guda goma.
Zaman ya bayar da dama ga mutane masu yawa daga kowane yanki sun bayyana korafin su a gaban majalisar da mahalarta taron ba tare da tsangwama ba kowa ya fadi albarkacin bakinsa kuma an dauki jawabin kowa .
Haka kuma majalisar ta kamanta adalci wajen dauko takardun mutanen da suka mika koken su, alhali wasu basu da zaton za a amince a kirasu don fitowa su bayyana raayin su game da abin da suka mikawa majalisar.
Muhawara mafi zafi itane wacce ta fito daga yankin Tafawa Balewa game da masarautar Sayawa chiefdom da sauran korafin masarautun hakimai da sauran su.
Read also: Shugaban Burkina Faso ya kori Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya Carol daga ƙasar
Ga Wani Labarin:GWAMNATIN JIHAR BAUCHI TA SOKE TAKARDUN FILAYEN KIWO DA AKA RABAWA MANOMA A DARAZO
Kusan kowace karamar hukuma ta jihar Bauchi an samu korafe-korafe game da masarautu da aka kirkiro a Yankin.
Manyan mutane da suka kunshi sarakuna da wakilan su da tsoffin ‘yan majalisa da tsoffin kwamishinoni da shugabannin kananan hukumomi da manya da kananan yan siyasa da sauran mutanen jihar Bauchi.
Sarakuna suma sun turo sakon neman gwamnati ta yi hattara kan wannan lamarin. Kamar yaɗda Alhaji Ibrahim Sule Sakataren masarautar Ningi ya zo da sakon maimartaba Sarkin Ningi kan masarautar Ningi da aka kirkiro hakimai aka ci yaki aka bar su da kuturun bawa.
Haka lamarin ya yi ta gudana yadda kowa ke zuwa da tarihin yankin sa da kuma irin wasoson da aka musu lokacin fito da wata sarauta a yanki ko masautar su.
Ga Wani Labarin:Daliban Jami’ar Aliko Dangote dake Wudil sun Karrama Shugaban Hukumar Karota
A takaitace dai wanda suka samu ci gaba murna suke yi Wanda kuma aka rage su bacin rai suke yi. An yi taron lafiya an gama lafiya saiko daga karshen taron an samu hayaniya daga mutanen Tafawa Balewa.




























