Connect with us

Hi, what are you looking for?

Lafiya

WATA MATA TA KONE KANTA A BAUCHI SABODA BATA SAMU GANIN DIYAR FIRAYIM MINISTA BA

Bauchi Mata
Bauchi Mata

WATA MATA TA KONE KANTA A BAUCHI SABODA BATA SAMU GANIN DIYAR FIRAYIM MINISTA BA

Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Wata mata mai matsakaicin shekaru ta rasa ranta bayan ta bankawa kanta wuta a gidan marigayi Firaministan Najeriya na Farko, Sir Abubakar Tafawa Balewa, da ke titin Ran a Bauchi.

Ga Wani Labarin:Bauchi: Ƙungiyar Fulani Sullubawa Sun Yi Alwashin Samar Da Haɗin Kai Don Ingantaccen Tsaro

Rahotanni sun bayyana cewa matar, wadda ake kyautata zaton tana da tabin hankali, ta isa gidan a ƙeke Napep da gallon din man fetur, ta nemi ganin Hajiya Yelwa Abubakar Tafawa Balewa, ‘yar marigayi Firaminista kuma shugabar hukumar kula da marayu da yara marasa galihu ta jihar Bauchi wato (BASOVCA). ko da aka shaida mata cewa ba ta nan a gida ne sai ta dawo bakin ƙofar gidan, ta kwararawa jikinta man fetur sannan ta kunna wuta.

Shaidu sun ce kukan da ta yi ya jawo hankalin jama’ar da suka yi ƙoƙarin kashe wutar, amma maimakon ya taimaka, sai lamarin ya ƙara ta’azzara. An garzaya da ita Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH), inda daga bisani ta ce ga garinku nan a sakamakon manyan ƙuna da sassan jikinta ya samu. A cewar shaidun gani da ido, kafin ta rasu ta bayyana cewa ta yi zaton ruwa ta zuba, ba man fetur ba a jikinta.

Ga Wani Labarin:Cire Kwamishinan ‘yansandan Kano tamkar kashe maciji ne ba’a sare kan ba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce kwamishinan ‘yan sanda Sani-Omolori Aliyu ya ba da umarnin gudanar da bincike. Ya ƙara da cewa bincike na farko ya nuna matar ‘yar wani marigayi Alƙalin kotun Shari’a ce, wadda ta taɓa yin aure da haihuwar ‘ya’ya, sannan matsalar tabin hankalin ta fara samun ta bayan haihuwar ɗanta na ƙarshe. Rundunar ‘yan sanda ta yi ta’aziyya ga iyalanta tare da addu’ar Allah ya ba su ƙarfin jure wannan mummunan al’amari.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...