Connect with us

Hi, what are you looking for?

Lafiya

ASIBITIN KWARARRU NA BAUCHI DA KE BACAS, NA FISKANTAR KALUBALE NA ADANA GAWA

Prof Mairiga CMD Bauchi Hospital
Prof Mairiga CMD Bauchi Hospital

BACAS

Daga Muazu Hardawa, Bauchi

Ganin yadda ake da saukin farashin adana gawarwakin mutanen da suka rasu a asibitin kwararru na Bauchi da ke BACAS, hukumar asibitin ta bayyana irin kalubale da take fiskanta saboda lalacewar na’urorin sanyi na asibitin a halin yanzu.

Profesa Mairiga Abdulkarim CMD wato shugaban asibitin shine ya bayyana haka cikin hirarsa da manema labarai a ofishin sa. Don haka ya kara da cewa a asibitin kwararrun na Bauchi suna da firjiin na’urarr sanyi da ake ajiye gawa guda 20 a asibitin, Amma 18 daga ciki sun lalace, sauran guda biyu da suka rage kuma basa aikin da ya dace idan an sa gawa a ciki sanyin baya gamsarwa daga bisani gawar tana lalacewa kwana kadan take fara wari daga waje ana ji.

Don haka ya ce Hakan na haifar da matsala saboda da rashin sanyin yana hana gawa tsantsamewa, don haka gawar mutane tana rubewa tana wari.

Ganin haka suka daina karbar gawar da ake kawowa saboda wasu ‘yan uwan suna kawo ajiye gawa suce zuwa gobe daga bisani su dauke kafa a rasa yadda za a yi da gawar har ta fara damun asibitin da wari.

A Iya Karanta Wanna:YAN BANGA DA MUTANE 19 SUN RASU A YAYIN ARANGAMA DA YAN BINDIGA A YANKIN DA GWAMNAN BAUCHI YA FITO

Dr. Abdulkarim Garba Mairiga ya Kara da cewa sun dauki wannan mataki ne don kare lafiyar rayayyu da tsabtar asibitin.

Musamman ganin Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir na jihar Bauchi ya bayar da kwangilar gyaran asibitin wanda nan ba da jimawa ba za a fara aikin, kuma za a gama cikin wata shida. Dakin adana gawarwakin wato motuary yana cikin wuraren da za a gyara, Kuma dukkan firiji 20 za a gyara su, Kuma da zarar an dawo cikin asibitin za a fara aiki da su a ci gaba da karbar gawarwakin mutane da ke bukatar ajiyewa ana adana musu.

Bincike da muka gudanar mun gano saukin ajiye gawa da gyara ko wanke gawa a asibitin na BACAS yadda ake karbar naira dubu biyu kwana daya shine ya sa wasu mutane musamnan kabilu sukan kawo ajiye gawa kafin daga bisani idan sun shirya jana’iza irin ta al’ada sukan dauka su tafi dasu garuruwan su don bisnewa.

Amma a asibitin koyarwa na ATBUTH kowane kwana guda da gawa za ta yi a firji ana biyan naira dubu bakwai ne Kuma a biya kudin gyara gawa, don haka mutane ke son kawowa asibitin kwararru na Bauchi.

Profesa Mairiga Abdulkarim ya ba mutane hakuri kan lamarin, saboda idan sun karbi gawa ba a zuwa a dauka a kan lokaci lamarin yana zama damuwa. Musamnan a wasu lokuta jami’an tsaro suna kawo gawa amma bincike don neman masu gawar yakan dauki lokaci a barsu da gawa babu mai ita har ta fara wari, Kuma bisa doka ba za su bisne ba sai an basu izini. Yin sutura wa gawar Shima sai sun kashe kudin likkafani da rami da abin hawa da sauran dawainiya.

Bayan haka idan kuma suna aiki da firji guda biyu don adana gawa biyu idan wasu sun kawo ance ba wuri Mai kyau shima mutane suna bata rai, wani lokacin har suga kamar an ki karba ne da gangan.
Yace kusan sau uku ana kawo musu gawarwakin daga jami’an tsaro amma rashin aikin wajen ajiye gawar ya sa suka fara wari kusan ta ko Ina aka fito ana jin wari, don haka suka bukaci su basu izini a musu janaza suka ki kuma suka ki zuwa suka ce suna binciken lamarin har ya kai ga an samu sabani suka ce za su dawo musu da gawar ofishin jami’an tsaron don ba za su bari mutane su cutu ba kafin daga karshe suka basu izini suka yi wa gawar janazar.

A Iya Karanta Wanna:Aikin Jarida/Ƴancin Jairda/Makomar Jarida

Amma ya bukaci mutane su ci gaba da kai . ajiye gawarwakin zuwa asibitin koyarwa kafin a gama aikin gyaran asibitin wanda da za a fara nan ba da jimawa ba.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...