Daga : Ahmed Zubaru Chedi (Ph.D)
Gaisuwa tare da girmamawa a gareka. Mai girma Gwamna ina da wasiƙu guda biyu zuwa gareka waɗanda suka shafi cirewa ma’aikata kuɗi daga albashin su ko sunaso ko basaso. Wasiƙa ta farko itace wannan wacce ta shafi KSCHIMA, sai kuma ta biyu da zata biyo baya amma yanzu zan fara da wannan, nan gaba kuma zan rubuto ta biyu akan Pension Contribution.
Mai Girma Gwamna Ni Ma’aikacin Gwamnatin Jihar Kano ne, ba ɗan siyasa ba kuma ban taɓa riƙe katin wata Jami’yar siyasa ba amma ina yin zabe kuma ina zabar mutum ne ba tare da la’akari da a siyasar da ya fito ba saidai a bisa yaƙinin cewa har ga Allah na yarda shine wanda yafi sauran abokanan takarar cancanta, kuma a lahira ina da hujjar da zan kare kaina a wajen Allah, wannan dalilin shi yasa bana goyon bayan Banbaɗanci ko Tumasanci a kowane irin mulki ne, domin a ranar lahira Allah zai tambayemu abun da muka aikata ko muka furta. Ina goyon bayan gaskiya daga kowane mutum ba tare da la’akari da Jam’iyar da ya fito ba, kuma ina ƙyamar rashin gaskiya ko cin Amana daga kowaye, shima ba tare da la’akari da Jam’iyar da ya fito ba.
Read also: BUƊAƊƊIYAR WASIƘA GA MAI GIRMA ƊAN MAJALISAR TARAYYA, MAZABAR GWALE
Duba da Hadissan Manzan Allah (SAW), cewa dukkanin ku makiyaya ne kuma za a tambaye ku abisa kiwon da aka baku, sai kuma daya Hadisin da yake cewa, duk wanda yaga abunki a cikinku to ya hana, gwargwadon ikon da yake dashi, walau da ƙarfin mulki, ko faɗa da baki domin a gyara ko kuma ƙyamatar Abun a zuciyarshi in bashi da ikon hanawa ko faɗar. Kasancewar ina da damar da zan faɗa domin sakon ya je wurinka shi yasa na biyo wannan hanyar domin bani da ikon ganinka. Ina ganin in nayi hakan na taimaka wajen sauke nauyin da al’umma suka ɗora maka ni kuma na sauke nauyin da ke kaina na faɗa maka gaskiya ko da kuwa abun bazai maka ko waɗansu maƙaranbanka ko masu goyon bayanka daɗi ba, tunda dai abun da na faɗa na faɗeshi ne tsakanina da Allah domin a gyara, da ace ina da damar da zan ganka fuska da fuska na gaya maka da bazan biyo wannan hanyar ta (Social media) ba.
Ga Wani Labarin:
SUBEB DA UNICEF DA UBEC SUN KADDAMAR DA GANGAMIN SA YARA MAKARANTA A BAUCHI
Mai Girma Gwamna nayi wannan shimfiɗa ne domin na san akwai waɗanda za su yimin fassara ko fahita daban bawai don abun da na faɗa ba gaskiya bane sai dai domin kare matsayin su a gwamnatinka ko abun da suke samu ta dalilin banbaɗanci da tumasanci da suke yi. Waɗansu kuma za su ce adawa na ke yi ko kuma shaci fadi ne kawai .Ba na tsoron duk wata fassara da za ayimin ko kuma tsoratarwa domin na fuskanci tursasawa da barazanar rasa aiki sakamakon rashin goyon baya da kuma bada haɗin kai domin Zaluntar Al”umar jihar Kano dangane da Filin Makarantar Kano State Polytechnic. Na faɗi haka ne ba don in yabi kaina ko na kwarzarta kaina ba, sai domin duk waɗanda zasu karanta wannan wasiƙa suyi min adalci. Akan adawa nakeyi ko kuwa gaskiya na faɗa.
Mai girma Gwamna mutane da yawa (wanda nima ina daga cikinsu) sun yarda cewa kana da kyakkyawar niya domin cigaban Jihar Kano, hakanan kuma kana sauraren kukan mutanen da kake shugabanta amma akwai waɗansu daga cikin maƙaranbanka da kuma ‘yan siyasa da suke kawo maka cikas ba domin komai ba sai saboda da son zuciya da biyan buƙatar kansu da kuma ta siyasar su.
Ga waɗanda basu sani ba ,shi dai tsarin Taimakekeniyar Lafiya na Jihar Kano (KSCHIMA ), an samar da shi tare da mayar da shi doka a ranar 17 ga watan Augusta 2016 amma bai fara aiki ba sai a ranar 20 ga watan Yuni (June ) 2018.
Daga wancan lokacin 20 ga watan Yuni 2018 (20th June 2018) zuwa yau Asabar 6 ga watan Satumba 2025 an cirarwa wa maaikantan jihar Kano kuɗi tsahon watanni 87 ga wanɗanda aka fara tsarin dasu har yanzu kuma suna karbar albashi. wanda a kowane wata kuɗaɗen da aka tara baya gaza Naira Miliyan Ɗari (₦100,000,000) a jimilla.
Bari in bada misali da kaina. A duk wata ana cirarmun ₦4000, a halin yanzu abun da aka ciranmu a tsahon wannan watanni 87 ya kama ₦348,000, amma dagani har iyalaina da muke kan tsarin (Gabaki daya mu 6) bamu ci moriyar wannan tsari da yakai ₦5000 a tsahon shekaru takwas ɗinnnan ko kuma watanni 87.
Ga yadda tsarin yake: A bisa dokar KSCHIMA ta 2016 shine a duk wata za a ciri kuɗi daga albashi ma’aikaci a turawa KSCHIMA.
A bisa wannan jadawali kamar haka;
01 – 04, ₦1,400
05 – 07, ₦1,600
08 – 12, ₦2,600
13 and above ₦4,000
Consolidated ₦5,500
State Assembly members ₦10,000
Commissioners, ₦8,000
Special Advisers ₦7,000
Senior Special Assistant ₦1,500
Special Assistant ₦1,400
Local Government Chairman ₦5,000
Vice Chairman ₦4,000
Elected supervisory Councilor ₦4,000
Local Government Secretary ₦4,000
Sau da yawa mutane za su je Asibiti ɓangaren KSCHIMA sai ace babu magani amma in ba a ɓangaren KSCHIMA bane wanda yake saya zaka yi sai ka samu magunguna kuma masu inganci, wannan a (Private) kenan, wato Asibitoci masu zaman kan su. A bisa dokar KSCHIMA ko da ba a samu magani ba a lokacin da kaje dole ne Asibitin su samar ma da magani cikin awanni 48, wannan shine dalilin da yasa ake karɓar lambar waya in kaje asibitin, domin a kiraka a baka maganin lokacin da aka samu.
Akwai asibiti wanda ba na gwamnati ba da na yi rijista da su (Private) tun 2015, in iyalena sukaje a matsayin KSCHIMA sai ace ba magani amma in sunje a Private sai a duba su sosai kuma a basu magunguna masu kyau. wannan ɗaya ne daga cikin dubunnai. Na canza asibiti daban-daban har guda uku domin rashin gamsuwa da tsarin, amma har yanzu bata sake zabi ba.
Ga Wani Labarin:
Read also: YADDA KOTUN DAUKAKA KARA TA SAUKE ABBA GIDA-GIDA, TA TABBATAR DA GAWUNA A MATSAYIN GWAMNAN KANO
Ƙarin Bayani Akan Tsarin Taimakekeniyar Lafiya ta Jihar Kano (KSCHMA)
Duk da cewar ana cirar min ₦4000 duk wata tun daga June 2018 amma ban fara cin moriyar tsarin ba sai a Shekarar 2023.
Naje asibitin da nake KSCHIMA saboda ina mura, amma abun takaici maganin da aka bani, ₦50 ake sayar dashi a unguwarmu. Allah ya sa ma ba takanas naje ba hanyace ta bi da ni na shiga asibitin. Dana lissafa in ace zan zuba mai a mota ta sai na kashe ₦2000 amma naje an bani maganin ₦50. wannan shine karon farko da naci moriyar KSCHIMA bayan bada gudunmawar sama da N200,000.a cikin watanni sama da 50. A takaice kowanne wata an cirarmin ₦4000 ni kuma naci moriyar ₦1 ɗaya kacal daga cikin ₦4000 da ake cirarmun
A saboda haka na canza asibiti saboda rashin gamsuwa da wancan. A shekarar 2024 iyalaina sunje sabon asibitin da na canza har sau uku lokaci daban-daban shima basu taɓa samun magani ba wannan asibitin shine Muhammad Abdullahi Wasai watau Asibitin Nassarawa
Daga bi sani na sake canza asibiti zuwa na kusa dani watau Imamu Wali, dake Janbulo, ba laifi wannan asibitin suna da kulawa kuma suna bada magani daidai gwargwado. Zai wahala kaje ace babu magani ko babu likita. Kash! sai dai suma sun shiga sahun masu cewa babu maganin, wanda a baya ba haka suke ba.
A watan Janairu 2025, ni da kaina, naje Asibitin Imamu Wali amma ban samu magani ko ɗaya ba, a watan Augusta 2025 iyalina sunje Imamu Wali shima basu sami magani ko daya ba. A ranar 3rd Satumba yarana guda biyu sun tashi da Maleria munje asibitin shima bamu samu magani ko ɗaya ba. A jiya Jummu’a 5th Satumba 2025 ni da iyalina mun tashi da mura da kuma yarinya yar shekara 16 munje asibitin amma sai aka bamu magann tari na yan shekara 8 zuwa 12. sauran kuma akace saidai mu dawo ranar Litinin ba a buɗe Store ba. saboda ana hutunun Mauludi.
Wani rahoto yanuna cewa a watan Afrilu na 2025 (April 2025) akwai yawan adadin ma’aikata, ba masu riƙe da muƙaman siyasa ba su 60,000. Kadan zamu ƙiyasta bisa kiyashin kowa a cirar masa ₦2,400, hukumar KSCHIMA ta sami Naira Miliyan Ɗari da Arba’in da Hudu (₦144,000,000) a watan April 2025, kawai. In har a wata ɗaya za a tara sama da Miliyan Ɗari to Miliyan nawa ake tarawa a shekara? kuma nawa ake kashewa marasa lafiya duk wata? Me akeyi da sauran kuɗin a zahiri ba a takarda ba.?
Mai girma Gwamna, ni, nasan waɗansu abubuwa da suke faruwa a KSCHIMA kasancewar ina daga cikin kwamitin kungiyar Kwadago da suka bibiyi aikin KSCHIMA a tsahon wata shida da fara aikinsu (November 2018), a lokacin mun gano abubuwa da dama, hakanan ina daga cikin waɗanda suka sami halartar taron karawa juna sani dangane da KSCHIMA (December 2021) nine ma na jagoranci wakilan da suka wakilci ma’aikatun da suka shafi bangaren Ilimi, kuma mun bada shawarwari ta yadda za a inganta tsarin amma ga dukkan alamu har yanzu akwai Runa a Kaba
Tabbas, mai girma Gwamna ina daga cikin waɗanda suka yarda kana da zuciya mai kyau, kuma kana da burin kawo gyara amma a gaskiya akwai daga cikin maƙarraban gwamnatinka, da waɗansu masu yima banbaɗanci waɗanda haƙiƙanin gaskiya ba suna sonka ne tsakani da Allah ba sai domin moriyar da suke samu daga gwamnatinka ko kuma suke sa ran samu, saboda haka baza su taɓa gaya ma gaskiyaba domin suma suna amfana da cin amanar da ake maka.
Mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf, ka shina a ranar lahira kowa ta kansa yake yi, kuma kowa zai tsaya a gaban Allah domin amsa tambayoyin abun da ya aikata. Saboda haka in kana sane da abubuwan da ake aikatawa amma kaƙi ɗaukar mataki, to Allah ya sani, in kuma baka sani ba to ya kamata ka bincika kuma ka ɗauke mataki domin kare kanka a ranar Lahira, Ranar da duk ƙaunar da Uwa takewa Ɗanta zata gudu ta barshi domin tsananin dake wannan rannan.
TAMBIHI:
Abun tambihi a nan shine. Mai girma Gwamna
1. Kasa idanu a harkar KSCHIMA
2. Ka fidda wani tsari da zai tuntubi ma’aikatan gwamnati domin jin koke -koken su da kuma shawarwarinsu dangane da harkar KSCHIMA
3. A bisa tsarin KSCHIMA duk waɗanda aka cirarwa kuɗi na KSCHIMA ana tura ₦400 kacal zuwa asibitin da ya buɗe file.
4. Akwai mutane da yawa waɗanda basu buɗe file ɗin KSCHIMA ba kuma duk wata ana cirar masu kuɗi, tunda basu buɗe file ba to kuɗaɗen su suna KSCHIMA, waɗanda suka bude file din sauran kuɗaɗensu yana KSCHIMA bayan an tura ₦400. Misali kamar ni ana cirarmin ₦4000 duk wata, za a tura ₦400 kawai sauran ₦3600 suna KSCHIMA. Ka bincika mai ake yi da ragowar kuɗin a zahiri ba a takarda ba
5. A binciken da muka gudanar a shekarun baya mun gano cewa ba ko da yaushe ne ake turawa asibitocin kuɗin ba.
6. A wancan lokaci akwai zargin badaƙala sosai a hukumar KSCHIMA.
7. Ka bincika Badaƙalar da ake zargi a wancan lokacin taci gaba ne, ko ta canza salo ne?
8. A bisa dokar KSCHIMA dole ne duk wani ma’aikacin gwamnatin jihar Kano ko mai rike da mukamin siyasa a gwamnatin jihar Kano sai an cirar masa kuɗin KSCHIMA ko yana so ko baya so shi kuma ya rage nasa da ya nemi asibitin da zai register dashi matuƙar asibitin yana cikin tsarin KSCHIMA. Abun tanbihi anan shine shin ana cirarwa masu riƙe da muƙaman siyasa ko kuwa sai dai ma’aikatan gwamnati kawai?
9. Akwai nau’in cututtuka daban-daban da wannan tsarin KSCHIMA ya tanada lokacin da aka kafa ‘Dokar KSCHIMA’ amma yanzu in kaje sai ace waɗannan cututtukan basa tsarin KSCHIMA, abun tambihi anan shine, KSCHIMA tana da damar canza tsarin da ‘Doka’ ta tanada ba tare da ankai dokar Majalisa anyi mata gyara ba? in kuma an yi gyaran dokar ne, to ya kamata a sanar da Jama’a domin su san yanayin cututtukan da zasu je a bisa tsarin KSCHIMA.
10. Mai Girma Gwamna, mai mulki baya sanin haƙiƙanin masoyansa sai lokacin da baya kan gadon mulki ko kuma bashi da wani matsayi da za a samu abun duniya a hannunsa.
11. Masu Banbaɗanci da Tumasanci basa so a gaya wa mai mulki gaskiya, in an faɗa ma sai suce adawa akeyi masa
12. A ranar Lahira babu boye – boye kuma kowa za a tambaye shi abisa amanar da aka ɗora masa. Gaskiyar mutum ce zata fidda shi . Duk wanda ya aikata alkhairi zai gani hakama in mutum ya aikata sharri shima zai gani.
Kamar yadda na faɗa a baya ni dai bani da ra’ayin kowacce Jami’ya ko wani mutum, ina goyon bayan gaskiya ne a duk inda take kuma ina kyamatar karya da yaudara daga kowaye kuwa.
Allah ya nuna mana Gaskiya ya bamu ikon binta ya nuna mana karya da yaudara ya bamu ikon kauce mata. Ya bamu ikon faɗin Gaskiya akan kowaye komai kuma Ɗacinta.
Read also: Yarjejeniyar Zaman Lafiya da Alero: Gaskiya Ko Wasan Kwaikwayo Da Rayukan Al’umma
Ma girma Gwamna ina yi maka addu’ar Allah ya baka ikon karɓar gaskiya da kuma aiki akan gaskiya, Allah yayi maka Jagora, ya baka ikon sauke nauyin dake kanka. Allah ya bayyana maka masoyanka na tsakani da Allah, ya nuna maka makiyanka na zahiri da na boye ya raba ka da makiyanka na zahiri da na boye. Ya baka ikon tabbatar da gaskiya da kuma adalci a mulkinka Ameen.
Ahmad Zubair Chedi.(Ph.D), Malami a Kwalejin Polytechnic ta jihar Kano.

Dr. Ahmed Zubairu Chedi




























