Daga Farouk Musa Isa
Kotun Daukaka Kara da ke Birnin Tarayya Abuja ta tabbatar da hukuncin da Kotun sauraron Korafin Za6en Gwamnan Jiha Kano ta yanke a kwanakin baya, a inda ta sauke Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da mayar da gurbinsa da Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC.
Alkalan Kotun Daukaka Kara su uku (3) sun tabbatar da cewa Gawuna shi ne ya samu nasara a za6en gwamna da aka yi a ranar 18 ga watan Maris, 2023.
Read also: Tsaftace Kundin Shirin AGILE na Kano: Abubuwan Da Aka Cire Da Wanda Aka Kara
Haka kuma, kotun ta ce Gwamna Yusuf ba halastaccen dan jam’iyyar NNPP ba ne a lokacin da ya tsaya takara da kuma lokacin da aka yi za6en gwamna a jihar a watan Maris.
Alkalan kotun sun yi dogaro ne da sashi na 177 na Kundin Tsarin Mulkin kasar nan, wanda yake cewa ‘Wajibi ne sai mutum ya zama dan jam’iyya kafin ya cancanci tsayawa takara” a Najeriya.
Daga nan sai kotun ta umarci Abba Yusuf da ya bai wa Gawuna Naira miliyan daya (N1,000,000) saboda bata masa lokaci da ya yi.
Hukuncin Kotun Daukaka Kara ba zai zama shi ne karshe ba, domin duk wanda bai gamsu ba, yana iya daukaka kara zuwa Kotun Koli.




























