Connect with us

Hi, what are you looking for?

RA'AYI

Tsaftace Kundin Shirin AGILE na Kano: Abubuwan Da Aka Cire Da Wanda Aka Kara

AGILE
AGILE

Daga Abba Rabiu Sarkin Fulani

ABUBUWAN DA AKA CIRE;

1. An cire dukkan hotunan da suka sabawa koyarwa addinin musulunci da al’adun mutanen Kano a cikin kundin, an maye gurbin su da wadanda suka dace ( Kano dress code).

2. An cire kalmar Gender-Based Violence, GBV (cin zarafin jinsi) an maye gurbintsa da ‘Safety and Security of children within and outside School’ wato (kare dalibai daga cutarwa a ciki da wajen makaranta), saboda kalmar GBV tana koyawa mata cewa, maza barazana ne a rayuwarsu.

3. An cire sadarar da ta baiwa mata yancin yin aikin gwamnati; “the right to work”.

4. An cire sadarar da ta baiwa yara ‘Yanci akan iyayen su.

5. An cire sadarar da ta baiwa mata ‘Yancin fita daga gidajen su a kowanne lokaci suka ga dama.

ABUBUWAN DA AKA KARA A KUNDIN;

1. Koyawa dalibai yadda ake alwala a aikace.

2. Koyawa dalibai yadda ake amfani da Aswaki da gawayi a wajen tsaftar baki.

3. Koyawa dalibai yadda ake tsarki a aikace.

4. Nusantar da dalibai cewa, lokacin da suke cikin jinin al’ada ba’a taba Al-Qur’ani mai girma da shiga masallaci da mu’amalar aure har sai bayan sunyi tsarki.

5. Koyawa dalibai sana’o’i da girmama iyayen su da mazajen su. Misali ‘Made in GGSS Unguwa Uku shoes & bags’ wato (kayayyakin da aka samar a makarantar sikandiren ‘Yan Mata ta Unguwa uku).

6. Za’a fassara kundin shirin AGILE zuwa yaren larabci da ajami.

An gudanar da taron karawa juna sani na kwana biyu (13-14 Disemba, 2023) wanda aka tsaftace kundin shirin AGILE a Kano.

A taron akwai wakilan Sarkin Kano da na Karaye da wakilan Majalisar Malamai da Majalisar Limaman Juma’a da HISBAH da FOMWAN da ASSUS da Shugabannin Iyaye da Malamai gatan Makaranta (SBMC) da ma’aikatan ma’aikatar ilimin jihar Kano da shugabannin shirin AGILE da yan jaridu da sauran su.

Kwamishinan ilimin jahar Kano, Hon Umar Haruna Doguwa ya halarci gurin inda ya gabatar da jawabansa. Sannan ya jaddada godiyar sa ga malaman jihar Kano bisa gudummuwar su akan tarbiyar al’umma.

Allah ya taimaki gwamnatin jihar Kano.

Abba Rabiu Sarkin Fulani
Mamba a Kwamitin Sake Duba Kundin AGILE.
(Daga 13 – 14 Disamba, 2023)
16 Disamba, 2023.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...