Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Amnesty ta zargi sojojin Najeriya da yin kisan gilla a yankin Kudu maso Gabas

Amnesty
Amnesty

Amnesty ta zargi sojojin Najeriya da yin kisan gilla a yankin Kudu maso Gabas

Daga Sunusi K/Na’isa

Amnesty International ta ce tana da kwararan hujjoji da suka haɗa da sunaye da adireshi na mutanen da ake zargin sojojin Najeriya sun kashe ba bisa ka’ida ba a yankin Kudu maso Gabas.

“Muna da shaidarmu kuma muna matuƙar farin cikin gabatar da ita, ko yaushe muna tuntuɓar iyalan waɗanda abin ya shafa kuma muna imanin cewa akwai buƙatar bincikar rayukan da aka kashe don bi musu hakin su.

“Bari mu zauna, mu duba wadancan shari’o’in, mu gano waɗanda suka aikata abin da kuma yaushe, sannan mu tabbatar da cikakken nauyin dokar domin tabbatar da adalci ga waɗanda abin ya shafa,” in ji Daraktan Amnesty International na Najeriya, Isa Sanusi, a cikin wani shiri na gida talabijin mai taken (Morning Brief) na Channels a ranar Juma’a.

A cikin sabon rahotonta mai suna ‘A Decade of Impunity: Attacks and Unlawful Killings’ a Kudu maso Gabashin Najeriya, kungiyar ta zargi ‘yan sandan Najeriya, sojoji, jami’an tsaro na yankin Ebube Agu, da wasu masu zaman kansu da ke cin zarafin bil adama a yankin.

Wasu daga cikin labarai:

Ƙididdiga rahoton ya tattara sunayen mutane da suka mutu sama da 1,844 tsakanin watannin Janairu 2021 da Yuni 2023, tare da shari’o’in azabtarwa, tilasta bacewar mutane, kama da wasu laifuka.

Sai dai Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, ya yi watsi da rahoton na Amnesty, yana mai jaddada cewa sojoji ba sa aikata kisan gilla a yankin Kudu maso Gabas ko kuma a ko’ina a Najeriya. Ya ce ayyukan tsaro a yankin sun rage ƙarfin masu aikata laifuka.

Sanusi ya yi watsi da iƙirarin da hedkwatar tsaro ta yi cewa ƙungiyar na kai wa sojoji hari akai-akai.

“Ina ganin abin da kakakin rundunar tsaron ya ce gaba ɗaya ba dai-dai ba ne, a cikin rahoton, mun kuma ambaci wuraren da aka kashe sojoji ko kuma aka kai hari a barikokinsu, ba wai batun daidaito ba ne wajen la’antar sojoji, abin da muke yi shi ne gaskiya, muna cewa muna da kararraki,” in ji shi.

Daraktan ƙungiyar na ƙasa ya ce yawancin kashe-kashen da aka yi ba tare da shari’a ba sun faru ne a lokacin da ake gudanar da ayyuka a yankunan da ake zargin ‘yan ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) ko kuma reshenta masu dauke da makamai, wato Eastern Security Network (ESN). A wasu lokuta, ana zargin mutane ne aka dauko su daga gidajensu ba a sake ganin su ba, in ji shi.

Ya kuma ƙara da cewa Amnesty ta yi hira da mutane 100 waɗanda galibinsu ido-da-ido a yankin Kudu-maso-Gabas, don bayar da rahotonta, kuma ta rubuta wa sojoji game da zargin, amma rahotanni sun ce ba su samu amsa ba, inda ta jaddada cewa ba su da komai a kan sojojin.

“A binciken da muka yi mun tattauna da mutane 100, 95 daga cikin su ido-da-ido a yankin Kudu maso Gabas, kafin mu fitar da rahoton, mun aika da wasiƙa ga rundunar soji muna sanar da su wannan zargi tare da neman duk wani bayani da zai taimaka mana mu fahimci yadda ayyukansu ke shafar ‘yancin bil’adama, ba mu samu amsa ba,” inji Sanusi.

Amnesty ta lura cewa ƙungiyar kare haƙƙin “ba ta da wani abu a kan sojoji. “Bayanan mu sun haɗa da waɗanda aka kashe ba wai sojoji kawai ba, har da ‘yan sanda da Ebube Agu, wanda wasu gwamnoni suka kafa don magance rashin tsaro amma ya zama kayan cin zarafi,” in ji shi.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...