Yan Daba Sama da 500 sun Tuba Tare da Ajiye Makamansu a Kano
Daga Sani Aminu
Read also: Hukumar Shari’a da Rundunar Yan sanda a Kano za su kawo karshen faɗan daba da kwacen waya
Gwamnatin Jihar Kano ta karbi tuban wasu matasa sama da 500 a Kano da suka ce sun yi bara’a da ta’addacin daba sun kuma zubar da makamansu a yau Litinin.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya shi ne ya jagoranci karbar matasan a wani gagarumin biki a madadin gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Bikin da aka gudanar a dakin taro na ma’aikatar Sufuri ta jihar Kano, ya samu halartar manyan mutane daga ɓangarori daban-daban.
Hukumar Shari’a da Rundunar Yan sanda a Kano za su kawo karshen faɗan daba da kwacen waya
Ibrahim Waiya, yace gwamna Abba Yusuf ne ya amince a rika gudanar da wannan taro domin tabbatar da cewar matasa sun rungumi zaman lafiya a jihar Kano, a wani shiri da gwamnatin ta kirkiro wato (safe corridor project).
Kwamishina Waiya wanda shine babban jami’in gudanarwa na kwamatin samar da zaman lafiya a jihar Kano,yace tsohon kwamishinan yan sanda na Kano CP Husaini Gumel ne ya samar da shi tun lokacin yana Kwamishina a Kano.
Daruruwan matasan da ake gani a yanzu, rukuni-rukuni ne da shugabannin ‘yan Daba da suka tuba, kuma kowanne a cikinku yana da mabiya ,wanda yace hakan ba gaggarumar nasara ce, in ji Waiya.
Ya ce ” A madadin gwamnatin jihar Kano, Kwamared Waiya ya yabawa matasan saboda rungumar zaman Lafiya da kuma kishin su na ci gaban Kano”.
Yace kasancewar Kano ce ke Jagorantar jihohin Najeriya a kowanne bangare,bai kamata a rika rikice rikicen Daba da kwacen waya da kuma aikata miyagun laifuka ba.
Read also: Rundunar Ƴan sanda ta Hana Goyo a Babur a Kano
Ya tabbatarwa da mahalarta taron cewa su kansu matasan sun gaji da ayyukan Daba da kwacen waya a Kano.
Kwamishinan yaɗa labarai yace gwamna Yusuf ya bada umarnin a fara tantance matasan da suka tuba domin basu dama a cikin ayyukan gwamnati sanann wasu a saka su cikin shirin samar da zaman lafiya da sauran tsare-tsare da aka samar musu gami da mayar da waɗansu makarantu domin samun ilimi mai inganci.
Haka zalika,Waiya yace akwai magungunan wanke zukata da hukumar NDLEA zata baiwa matasan da suka tuba dan warkewa daga abinda suka samu kansu a ciki a baya.
Daga nan kwamishinan ya roki yan Dabar da su rike tubansu da kyau tsakaninsu da Allah sannan su zamo mutanan kirki.
Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi na II ya samu wakilcin Sarkin Shanun Kano, Alhaji Shehu Muhammad Dankadai.
A jawabinsa kwamishinan ‘yan sanda na Kano CP Ibrahim Adamu Bakori, Yace bayan zuwansa Kano ya fahimci cewa ana shan kwayoyi da kwacen waya da miyagun ayyukan Daba.
CP Bakori yace wannan ta sa ya samu gwamna Yusuf domin tabbatar da samar da shirin rungumar zaman lafiya a Kano domin magance matsalar.
Yaɗuwar Sankarar Mama: Mata 500 Sun Kamu a Kwana 210 – TMP. Adamu Yusuf
Kwamishina, ya nuna farin cikinsa da shirya taron, yana mai cewa abinda gwamnatin Kano ta kirkiro abu ne mai kyau kuma abin yabawa. Haka kuma ya godewa matasa abisa ajiye makamansu da su kayi.
Read also: Ƴan Sandan Kano Sun Daƙume Ƙasurgumin Mai Garkuwa Da Mutane
Kwamatin samar da zaman lafiyar na ‘Safe corridor project’ ya kunshi,wakilai daga kowanne bangare da suka halar da shugabannin gargajiya da ma’aikata da jami’an tsaro da mataimakin Shugaban jami’ar Northwest Farfesa Muktar Atiku Kurawa da Kwamishinan ‘yan sanda na Kano CP Ibrahim Adamu Bakori da Alhaji Gidado Muktar da sauransu.
Idan za a tuna a zamanin mulkin tsohon Gwamnan Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya gudanar da makamancin wanna shiri, in da aka samar da sulhu tsakanin manyan yan tauri a jihar nan wanda ya zama mabulin zaman lafiya a jihar. Amma a yanzu abin takaici lamarin ya na nema ya gagari kundila.




























