Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane sama da 100 a jihar Texas ta Amurka
Daga Yazid S Yahaya
Read also: Mutane 12 Sun Hallaka A Yayin Da Wasu Suka Jikkata A Haɗarin Mota A Kano
Fiye da mutane 82 alƙaluma ke nuna cewa sun rasa rayukansu a jihar Texas ta Amurka sakamakon ambaliyar ruwan da aka fuskanta a wani yanayi da hukumomin yankin ke cewa yanzu haka sun mayar da hankali wajen laluben gomman waɗanda suka ɓata a dalilin iftila’in wanda ya faru a lokacin da jama’a ke tsaka da wani bikin shaƙatawa.
Shugaban wata hukumar birnin Kerr ville yankin da ya fi fuskantar iftila’in Dalton Rice, ya shaida cewa suna ci gaba da gano gawarwakin mutanen da suka rasu sanadiyar ambaliyar.

Ambaliyar ta bazata, ta faru ne sakamakon zubar ruwan sama kamar da baƙin ƙwarya da aka shatata a tsakiyar jihar tun a ranar juma’a ana tsaka da bikin shaƙatawar, inda ruwa milimeta 300 ya zuba a awa guda, kwatankwacin sulusin ruwan da suke samu a shekara, lamarin da ya sa ruwan ya cika kogin Guadalupe da mita 8 a cikin minti 45 kacal.
Read also: Mazauna Kusa Da Madatsar Ruwa ta Ghari Da Su Yi Nesa Da Kogi – Inji Shugaban Ƙaramar Hukuma
Mummunan hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 21 a yau Lahadi a Kano
Shugaban Amerika Donald Trump ya ayyana dokar ta ɓaci a garin na Kerr Ville don gaggauta isar da kayan agaji da ake bukata, Inda a halin yanzu haka sama da ma’aikatan agaji 400 daga ƙungiyoyi sama da 20 ke aikin taimakon jama’a.
An saka jirage masu saukar angulu da jirage marasa matuƙa don nemo mutanen da ruwa ya tafi da su.
Bayan ɗan janyewar ruwan a dandalin da matasan suka taru, abun ba kyan gani, yanayin wurin ya hargitse, gwamman motoci a maƙale, wasu a saman bishiyoyi.
Paparoma Leon XIV ya nuna alhininshi kan iftila’in a jiya Lahadi tare da isar da ta’aziyyarsa ga iyalan mamata musamman yara ƴan mata da ke wajen babban bikin.
Read also: Karo na Biyu: Kimanin Kayan Abinci na Sama da Naira miliyan 42 aka Rabawa Kungiyoyi a jihar Kano
Ko a ranar Lahadi masana yanayin zubar ruwa sun shaida cewa akwai yiwuwar samun ruwan da zai kai daga milimetre 50 zuwa 100, a yankin har yana iya kaiwa milimetre 250.(rFi)



























