Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Mummunan hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 21 a yau Lahadi a Kano

Kano
Kano

Mummunan hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutane 21 a yau Lahadi a Kano

Daga Sunusi K/Na’isa

Akalla mutane 21 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu uku suka samu raunuka daban-daban a wani hatsarin mota da ya afku a Kasuwar Dogo da ke Dakatsalle a kan hanyar Zariya zuwa Kano.

Kwamandan hukumar FRSC reshen jihar Kano, Mista Muhammed Bature, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Abdullahi Labaran ya fitar ranar Lahadi a Kano.

A Karanta Wanna:Iftila’i: Yara Biyu Sun Mutu Sakamakon Mamakon Ruwan Sama

Bature ya ce hatsarin ya rutsa da motoci biyu. Trailer DAF mai lamba GWL 422 ZE, da Toyota Hummer Bas mai lamba KMC 171 YM.

“Mun samu waya da misalin karfe 08:23 na safiyar Lahadi, da samun labarin, sai muka yi gaggawar aika jami’ai da motar zuwa wurin, musabbabin faruwar lamarin ya faru ne sakamakon karya hanya da direban motar Toyota Hummer Bas ya yi, wanda ya kai ga karo da tirelar, wuta ta kone motocin duka biyun. An kai waɗanda lamarin ya rutsa da su zuwa babban asibitin Garun Malam domin kula da lafiyarsu,” inji shi.

Kwamandan sashin ya nuna matukar alhininsa kan wannan mummunan lamari da ya faru tare da mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamacin.

Bature ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka jikkata cikin gaggawa. Ya yi kira ga masu amfani da hanyar da su bi ka’idojin tuki, musamman kaucewa gudun wuce gona da iri da keta hanya da tafiye-tafiyen dare.

A karanta Wanna:Masu Zanga-zanga sun ƙone Fadar Sarki da ofishin hukumar NDLEA ƙurmus a jihar Kwara

Ya yi alkawarin tabbatar da tsaron masu amfani da hanyar. Sannan ya bukaci masu tuki a kan manyan tituna da su kasance masu lura da bin doka da oda. (NAN)

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...