Iftila’i: Yara Biyu Sun Mutu Sakamakon Makokkon Ruwan Sama
Daga Sani Auwalu
Read also: Maniyata aikin Umara daga Indiya mutum 42 sun mutu sakamakon hatsarin mota a Saudia
A ƙalla yara biyu sun rasa ran su sakamakon ruwan sama da aka tafka kamar da bakin ƙwarya a Minna babban birnin jihar Nija.
Ruwan sama da aka yi a ranar Talatar da ta gabata shi ya haifar da ambaliyar madatsar ruwa ta Tunga dake Mina.
Tsautsayi ya rutsa da yarinya ‘yar salin jihar Edo mai kimanin shekaru tara da kuma yaro namiji da har ya zuwa yanzu ba a tanttance asalin inda ya fito ba wanda aka sami gawar sa a magudana ruwa.
Read also: Sahihin Labari Ke Tabbatar Da Amincewar Jama’a, Ba Gaggawar Wallafa Ba- Shugaban NUJ
A karanta:Masu Zanga-zanga sun ƙone Fadar Sarki da ofishin hukumar NDLEA ƙurmus a jihar Kwara
Ganau, ya ce yarinyar tana tafe da ‘yar uwarta mai shekaru 11, domin zuwa sayen kayan miya sai ta zame a inda ta faɗa magudana ruwan, duk ƙoƙarin da ‘yar uwar ta yi na samun ceto yarinyar abin ya faskara. Daga bisani an sami gawar ta a magudanar ruwa dake Mandela tsahon kilomita biyar daga inda ruwan yai awan gaba da ita, ita ma ɗaya gawar an sameta a wannan guri.
Read also: Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
A karanta:Shugaban ‘Yan Bindiga Bello Turji Na yunƙurin Miƙa Wuya Bayan Mutuwar Yelo Danbokolo
Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Nija (NSEMA) ta tabbatar da samun gawawwakin kuma ta ce za ta ziyarci gidan mamatan domin jajanta musu da kuma basu tallafi, tare da cigaba da binciken iyayen ɗaya yaron.




























