Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Bashi Ko Ceton Rai? Kukan zuci da Siraɗin da Ma’aikatan Gwamnati ke ciki a Nigeria

Dr Ayagi
Dr Ayagi

Bashi

Daga

Dr. Murtala Iliyasu Ayagi

Suna shigowa ofis kowace safiya da takalmi mai sheƙi, riga a zanzare, da fuska mai cike da fata. Suna sa hannu a rajista, suna zaune a kan kujeru tamkarkomai yana tafiya lafiya. Amma baya ga waɗancan kayan ofis da murmushi na yarda, akwai kukan zuci. A gaskiya ma’aikatan gwamnati a Najeriya na cikin mawuyacin hali na bashi, kuma rance ya zama hanyar da kawai suke rayuwa da shi.

A ƙasar da hauhawar farashi ke gudu tamkar mahaukaci yayin da albashi ke tafiya kamar maciji, ɗan ma’aikaci yana barin gidan sa kullum cikin rashin tabbas tsakanin rayuwa da lalacewa. Albashin wata baya isa biyan kuɗin haya da kuɗin makaranta da na sufuri, da abinci. A gaskiya, ga mafi yawansu, albashin na shigowa banki ne kawai don a cire bashin rancen da aka karɓa daga ƙungiyoyin haɗin kai da ƙanana da matsakaitan bankuna ko kuma daidaikun masu ba da bashi mai tarin kuɗin ruwa ba tare da tausayi ba.

Wannan ba wai matsala ce ta kuɗi kawai ba. Matsala ce da ta shafi hankali da kuma zuciyar ɗan adam.

Ka Karanta:Amurka ta gargadi ‘yan ƙasarta su ƙauracewa gine-ginen gwamnati da kuma sashin da sojoji suke a Abuja

Dawainiyar Bashi

Ka ziyarci kowanne ofishin gwamnati a yau, za ka ji mutane na cewa: “Na karɓi loan ne, zamu iya ci gaba da rayuwa.” Rance yanzu ba don kafa kasuwanci ake karɓa ba, ko don gina gida. Ana karɓa don sayan abinci kawai ko don biyan kuɗin makaranta ko don biyan magani ko kuma don yin bukukuwa na addini cikin.

Ga wasu, rance ya zama kamar sarkar da ba ta da ƙarshe. Rance a kan rance. Lokacin da albashi ya zo, sai a ɗebe mafi yawan kuɗin ga wanda ya ba da bashi – abin da ya rage kuwa bai isa komai ba. Wasu ma sai su ƙara ɗaukar wani sabon bashin don su cike gibin da ya rage wanda hakan ke sa su shiga cikin rijiya marar tushe na damuwa da hauhawar ribar bashi.

Tasirin Hankali

A baya ga wannan kallon da ake yiwa ma’aikaci akwai kwakwalwa da zuciya cike da damuwar biyan bashi, alhakin iyali, da tsoron a kai su gaban ƙungiyar bashi ko a cire su daga aiki. Wasu sun kamu da ciwon zuciya da tashin hankali ko ma rikicewar kwakwalwa. Akwai labarai masu tayar da hankali na ma’aikata da suka fadi ko suka kamu da cuta saboda yawan tunani ko ma yunkurin kashe kansu saboda katuttun bashi da ya taru a kansu.

Aikin gwamnati wanda da can ake ganin da mutunci da sadaukarwa ga ƙasa, yanzu ya zama hanyar wahala da fargaba. Ma’aikaci na jiran albashi ba wai don ya ci ribar sa ba, sai dai don sanin yadda za a raba abin da ya rage. Su na numfashi, amma ba sa rayuwa. Su na aiki, amma ba su da ƙarfin zuciya.

Tsarin da Ya Lalace

Wannan matsala na nuna yadda tsarin ya tabarbare, tsarin da ba ya iya biyan albashi mai tsoka, amma yana cajin haraji mai yawa, kuma yana barin ma’aikaci a hannun ‘yan jari hujja. Yaya gwamnati za ta cigaba idan waɗanda ke mata hidima suna cikin halin talauci da bashi?

Ma’aikata su ne ake sa ran za su aiwatar da manufofin gwamnati da kula da al’umma, da koya wa yara a makaranta. Amma yaya mutum zai gudanar da aiki yayin da cikinsa ke fama da yunwa kuma zuciyarsa na cikin firgici?

Hanyar Warwarewa

Gwamnati ta tarayya da ta jihohi da Ƙanana hukumomi dole su tashi tsaye. A sake duba albashi. A koyar da ma’aikata dabarun sarrafa kuɗi. A tabbatar da kulawa da tsarin rance daga ƙungiyoyi da bankuna. Kuma a rufe ko a hukunta waɗanda ke amfani da manhajar bada rancen (loan App) marasa ƙa’ida.

Mafi mahimmanci, a dawo da mutuncin ma’aikaci. Mutumin da ke hidima wa ƙasa bai kamata ya zama baran bashi don ya ciyar da iyalinsa ba.

A ƙarshe, wannan matsala ba wai ta tattalin arziki ba ce kaɗai – matsala ce ta ɗabi’a da rashin adalci. Kuma ya kamata mu tambayi kanmu a matsayin al’umma: idan waɗanda ke hidima wa ƙasa ba sa iya rayuwa, to wa suke hidima a zahiri?
Allah ya kawo mana ɗauki, Amin.

A Karanta Wannan:Da ɗumi-ɗumi: Minista Wike ya ce masu ido da kwalli sune matsalar Abuja

Dr. Murtala Iliyasu Ayagi, Malami a Kwalejin Malam Aminu Kano, dake koyar da ilimin addinin Musulinci da Shari’a. Za a same shi ta kafar sadarwar email: murtalailiyasuayagi@gmail.com

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...