Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Rashin Tallafin Kuɗi Nijeriya Tai Asarar Gangaran a Fanin Kwamfuta, Prof. Roko

Farafesa Abubakar Roko
Farafesa Abubakar Roko

Rashin Tallafin Kuɗi Nijeriya Tai Asarar Gangaran a Fanin Kwamfuta, Prof. Roko

Daga Adita

 

Farafesa. Abubakar Roko na Jami’ar Usman Dan Fodio Sokoto, gangaran bangaren sanin ilimin na’ura mai kwakwalwa (Computer Science) da ake nemawa Tallafin Kuɗi domin kai shi ƙasar waje domin neman magani Allah ya karbi abinsa.

Kwanaki kadan cikin satin nan ake ta nema masa taimakon naira Miliyan goma sha uku (13,000,000) domin fitar da shi kasar Egypt a yi masa magani sakamakon ya jima a kwance ba shi da lafiya, ga kuma rashin abin hannu.

Tsawon kwanaki ana ta tallata asusun banki (Account No.) ɗinsa tare da hotonsa ana nema masa tallafi daga duniya amma kuɗin ba su hadu ba. Duk da an rawaito cewa Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya bayar da naira Miliyan biyar shi kadai tallafi daga aljihunsa. Allah ya sakamasa da alkhairi.

A halin yanzu Allah Ya amshi rayuwar Farfesa Abubakar Roko.

A Iya Karanta Wanna:Hafsan Sojoji Burtai Ya Kai da Kyar Sakamakon Harin ‘Yan Boko Haram A Borno

Muna Addu’ar Allah Ya gafarta masa Allah Ya sa Aljannah makomarsa.

Hakika fa gani ga wane Ya isa wane tsoron Allah! Ya kamata malaman Jami’a, da sauran ma’aikatan Gwamnati su sake gyara takunsu, bayan aikin nan na Albashi a kuma sake neman hanyar rufa wa kai asiri. Wannan lamari dole rayuwar ta nuna haka, babu yadda za a yi.

Duk da rai a gun Allah ya ke, kuma yana karbar ran duk wanda ya so ba tare da ƙarin ko da sakan na minti ba idan lokaci ya yi. Amma musilinci ya nunar da cewa a nemi magani ko da kuwa rai yana gargara.

Toh amma abin tambayo duk da muhimmanci wanna bawan Allah, ina Jami’ar da yake wa aiki, ina hanshaƙan masu kuɗin da ake da su haka kuma ina ƙungiyar ASUU?

Na tabbatar wanna kuɗin ba su taka kara sun karya ba. Miliyan sha uku (₦13,000:000) da basu fi a bawa mawaki ko ayi ɗiƙi a gurin aiki ba ko kuma a biya kuɗin hotel ba. Amma gashi an ƙi tallafawa mutumin da ya ke samar da        ɗaruruwan matasa da a yau duniya ke alfahari da su.

A Iya Karanta Wanna:Kungiyar RATTAWU Reshen Jahar Kano na Ta’aziya Ga ‘Yan Wasan da Suka rasu Sanadiyar Haɗarin Mota

Ya kamata shugabannimu su rinka tausayin al’umma tare da kyautata wa. Allah ya kyautata makwanci Shehin Malami-Roko.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...