NNPCL
…. Za mu dawo da aikin binne bututun gas daga Ajaokuta zuwa Kano…
Read also: Ban taɓa cin haram ba a shekaru 35 a aikin Gwamnati a Najeriya, in ji Barista Mainasara Kogo
Shekaru biyu bayan ƙaddamar da aikin haƙo ɗanyen man fetur a iyakar jihohin Bauchi da Gombe – wanda tun daga wancan lokaci ba a ci gaba da aikin ba, a yanzu sabon shugaban kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), Bayo Ojulari ya ce kamfanin zai koma bakin aiki.
Aikin da aka ƙaddamar a gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da ta gabata, ya sanya al’ummar arewacin ƙasar sun fara kyakkyawar fatan cewa yankin zai bi sahun wasu yankunan ƙasar da ke samar da man fetur wanda tattalin arzikin ƙasar ya dogara a kai.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya suke cigaba da kokawa kan tsadar rayuwa, wadda ke da alaƙar tashin farashin man fetur a sanadiyar cire tallafin da gwamnati ke bayarwa a ƙasar.
A jawabin Shugaban Najeriya Bola Tinubu na farko bayan rantsuwar kama mulki ya sanar da cire tallafin man fetur lungurungun a ƙasar.
Wani Makamancin Labarin:Gidauniyar Dangote Ta Kaddamar Da Rabon Abinci Na Naira Biliyan 16 Ga Talakawan Nijeriya
Tun daga lokacin ne farashin man fetur ɗin ya fara tashi, wanda kamar yadda aka saba, farashin kayayyaki da kuɗin sufuri da sauran abubuwa suma suka tashin Gwauron zabi a faɗin ƙasar.
Tallafin Man Fetur
Shi dai tallafin man fetur ɗin nan wasu kuɗaɗe ne da gwamnatin tarayya ke fitarwa domin biyan wani ɓangare na kuɗin da ake kashewa wajen sayowa da shigo da tataccen man fetur daga kasuwannin duniya zuwa Najeriya tare da sufurinsa zuwa jihohi domin ƴan ƙasar su same shi a farashi mai rahusa.
Hakan ya sa ƴan arewacin Najeriya suka shiga murna da farin cikin ganin za a fara haƙo ɗanyen man daga yankinsu, wanda hakan zai sa su same shi ba tare da wahalar sufuri ba.
Read also: Chanza Takardar Naira Zai Kawo Ƙarshen Rike Kuɗi a Hannun Yan ta’adda a Najeriya -Ado Dansudu
Idan za a tuna, a ranar Talata 22 ga watan Nuwamban shekarar 2022 ce shugaban Najeriya na wancan lokacin, Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin haƙo ɗanyen man fetur a yankin Kolmani da ke iyakar jihohin Bauchi da Gombe da ke arewa maso gabashin ƙasar, wanda shi ne karon farko da aka fara aikin haƙar man a arewa.
Haka kuma bayan wannan, kamfanin na NNPCL ya bayyana cewa a cikin watan Maris na 2023 ne za a fara aikin haƙo ɗanyen man fetur a jihar Nassarawa da ke arewa ta tsakiyar ƙasar.
Sai dai tun daga lokacin, sai aka ji shiru, tamkar an akiki bawa garin su, har aka yi zaɓe sabuwar gwamnati ta fara aiki, lamarin da ya sa wasu ƴan yankin suka fara tambayar ko dai dama an ɗanɗana musu zuma a baki ne kawai.
A game da wannan ne sabon shugaban kamfanin NNPCL, Injiniya Ojulari ya ce ƴan yankin su kwantar da hankalinsu domin za su koma bakin aikin kamar yadda ya bayyana a tattaunawarsa da BBC.
A cewarsa, “Za mu cigaba da aikin haƙo mai a Kolmani da sauran wurare. Bayan aikin haƙo man, za mu kuma tabbatar da cewa mun gama aikin bututun man gas daga Ajaokuta zuwa Kano,” in ji shi.
Ya ce waɗannan ayyukan za su sa a sake buɗe kamfanonin da aka kulle a baya domin su cigaba da aiki sannan a buɗe wasu sababbi.
“Wannan zai sa a samu amfani a yankin, wanda zai kai ga kowa ya ci moriyarsa saboda arziki zai bunƙasa. Don haka dole ne za mu koma mu cigaba da wannan aikin,” in ji shugaban na NNPCL.
Ojulari ya ƙara da cewa shi ma ɗan arewa ne, inda a cewarsa ya yi mamakin martanin da wasu ƴan yankin suka riƙa yi lokacin da aka sanar da naɗa shi.
Read also: JAMB ta Dakatar Da Karatun Digirin Haɗaka Tsakanin Jam’i’o’i da Kwalejojin Ilimi A Najeriya
Wani Makamancin Labarin:ASIBITIN KWARARRU NA BAUCHI DA KE BACAS, NA FISKANTAR KALUBALE NA ADANA GAWA
Sai ya buƙaci ƴan yankin da ma ƴan ƙasar baki ɗaya da su ba shi goyon baya, kuma su taimaka masa da addu’a domin ya samu nasarar ciyar da yankin da ma ƙasar gaba.




























