Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Masarautar Rano ta Naɗa Nasiru Fargai a Matsayin Sakataren Yada Labarai

Mal. Nasiru Faragai
Mal. Nasiru Faragai

Rano

Mai Martaba Sarkin Rano, Ambasada Dakta Muhammad Isa Umaru, ya amince da naɗa Malam Nasiru Habu Faragai a matsayin mai magana da yawun Masarautar.

Sarkin ya sanar da hakan ne ta cikin wata sanarwa da Malam Nasiru Habu Faragai ya sheda wa kafar sadarwarmu ta STENTORNEWS.

Ka iya karanta wanna:Ko Kasan Sabbin Kwamishinonin Da Gwamna Kano Abba Yusuf Ya Naɗa?

Mai martaba Sarkin Rano ya ce masarautar ta duba dacewar naɗa Nasiru Faragai a matsayin Sakataren yaɗa labarai, duba da irin gogewarsa a fanin sadarwa gami da kwarewar da yake da ita a matsayin sa na tsohon ma’aikacin gwamnati kuma gogagge a fanin aikin yaɗa labarai, gami da gudunmawar da ya bayar na daga darajar masarautar a idon duniya.

Mai martaba Sarkin Rano ya ce “Mun naɗa ka ne saboda yaƙinin da muke dashi na zaka iya aikin da zai dace da kyakkyawar al’adar Masarautarmu, a saboda haka muna horonka da ka haɗa-kai da sashen yaɗa labaran shiyyar Rano dama sauran ma’aikatan yaɗa labaran masarautar domin ci gaba da ɗaga martabar masarautar da ma yankin a idon duniya baki ɗaya”.

Ka Iya Karanta Wanna:Horon Tukin Mota: Shugaban Karamar Hukumar fagge Salisu Masu Yayi Kira Ga Matasa Su Amfani Damar

Kafin ya bar aiki Nasiru Habu Faragai ya zama jami’in yaɗa labarai a kanana hukumomi daban-dabam, kamar Gaya da Ajingi da Sumaila da Albasu da Dala da Gwale da Doguwa da sauran su.
Haka kuma ya samu halartar Jami’ar Bayero ta Kano inda ya samu shedar karatun aikin jarida a matsayin matakin Diploma. Daga bisani ya yi ritaya bayan ya shafe shekaru 35 yana aiki. Ya kuma bar aikin a matsayin jami’in yaɗa labarai na shiryar Karamar Hukumar Wudil a ma’aikatar yaɗa labarai ta jihar Kano.

Sanarwar ta ce naɗin Nasiru Fargai a matsayin Sakataren yada labaran, na da alaƙa da yadda ya shafe tsawon lokaci yana bawa masarautar gudunmawa a fanin yaɗa labarai. Mai martaba Sarki ya ta ya shi murna da fatan Allah ya kama.

← Back

Thank you for your response. ✨

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...