An Bukaci Gwamnan Kano Ya Kori Kwamishiniyar Jin Kai Bisa Zargin Cin Zarafi
Ƙungiyar Likitoci ta ƙasa reshen jihar Kano ta yi kira ga Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya gaggauta korar Kwamishiniyar Jin Kai da Walwalara Jama’a ta jihar Hajiya Amina Abdullahi wato Amina HOD nan da awanni 48 bisa zarginta da cin zarafin wata likita.
Read also: ICPC Ta Kama Dan Jaridar Bisa Zargin Damfara Ta Naira Miliyoyin 14
Read also: Ɗan Jarida Zai Gurfanar da Hadimin Gwamna Kano a Kotu, Sakamakon Zargin Cin Zarafi
Shugaban Kungiyar Dr. Abdurrahman Ali ya shaida wa Freedom Radio cewa suna zargin Kwamishiniyar da cin zarafin wata likita Dr. Nusaiba Mahmud a lokacin da take tsaka da aikinta a sashen bada agajin gaggawa na ɓangaren yara na Asibitin Murtala a ranar Jumu’ar da ta gabata.
A wani bidiyo da likitar ta fitar ita ma ta bayyana yadda ta sha da ƙyar inda ta ce, Kwamishiniyar ta haƙiƙi ce tana iƙrarin cewa koda ita ƴar Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ce to sai ta ɗanɗana kuɗarta.
A Iya Karanta Wanna:An Buƙaci Mutane Su Fito Gwajin Hawan Jini da Ciwon Siga
Game da wannan zargi Freedom Radio ta tuntubi Kwamishiniyar Jin Kan ta Kano Hajiya Amina HOD amma koda aka soma yi mata bayani ta wayar tarho sai ta kashe wayar, daga nan muka sake kiranta amma an saka wayar a ‘Forward”, hakan ce ta sa muka aika mata da sakonnin kar-ta-kwana amma har kawo lokacin da muke hada wannan rahoton bata amsa ba.
A Iya Karanta Wanna:NDLEA Ta Kama Miyagun Kwayoyi Na Sama Da Naira Biliyan 16
A gefe ɗaya kuma Gwamna Kano Abba Yusuf ya karbi korafin ‘ya’yen kungiyar tare da umartar Kwamishina Ma’aikatar Lafiya ta jiha Dr. Abubakar Labaran Yusuf da ya hanzarta bincikar lamarin, wanda tuni aka kafa kwamiti domin duba batun.




























