Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce sai nan da ranar 12 ga watan Nuwamba Jihohin Arewa 17, za su fita daga cikin duhu.
Ministan Lantarki na kasar Adebayo Adelabu, ne ya bayyana hakan a jiya Talata, inda ya ce wutar yankin ba zata dawo yadda take a baya ba har sai ranar 12 ga watan Nuwambar mai zuwa.
Ministan ya furta hakan a yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan Majalisar Dattawan Najeriya, sai dai kuma zancen nasa yai kama da harshen sami, inda kuma ya ce za’a fara samun Wutar Kadan-kadan nan da Kwanaki 3 masu zuwa, kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.
Read also: “Babu Wani Dalilin da Zai Sa Na Yi APC”, Wanna Wasan Fulani Ne da Kanuri – Sule Lamido
Kana iya karanta:
IMF Ta Ce Bata Da Hannu A Janye Tallafin Man Fetur A Nijeriya
Read also: Mazauna Kusa Da Madatsar Ruwa ta Ghari Da Su Yi Nesa Da Kogi – Inji Shugaban Ƙaramar Hukuma
Toh, idan za a tuna a baya Gwamnatin tarayyar ta ce tana yin dukkan mai yiwuwa wajen ganin anyi aikin gyaran wutar lantakin nan da kankanin lokaci, ta yadda jihohin Arewan dake cikin duhun zasu ci-gaba da samun wutar kamar yadda suka saba.
A karshe Ministan ya bada tabbacin cewar Jihohi 17 na Arewacin kasar, za su ci-gaba da kasancewa cikin duhu har zuwa ranar Talata, 12 ga watan Nuwambar shekarar 2024.
Kana iya Karanta:
Read also: Ansamu Koma Bayan ‘Yancin Gudanar Da Aikin Jarida a Faɗin Duniya A Shekaru 5 – Rahoton IEAD
Irin waɗannan zantuka masu cin karo da juna su suke kawo shaku ga jama’a na ko ƙasar mu Nijeriya zata koma kamar yadda aka santa a baya na zama gwarzo Afrika?




























