Connect with us

Hi, what are you looking for?

Tsaro

Akalla Mutane 20 Sun Hallaka Ya Yin Da Suke Tserewa Farmakin ‘Yan Bindiga a Zamfara

'Yanbindiga
'Yanbindiga

Akalla Mutane 20 Sun Hallaka Ya Yin Da Suke Tserewa Farmakin ‘Yan Bindiga a Zamfara

Daga Wakilinmu

A kalla sama da mutane 20 ne aka ce sun rasa rayukansu a yankin Kali dake karamar hukumar Gumi a jihar Zamfara a Najeriya, yayin da suke tserewa daga farmakin ‘yan bindiga.

Majiyar STENTORNEWS ta ruwaito cewa mutanan sun hallaka ne bayan hawansu kwale-kwalen domin neman kubuta daga kisan kan-mai-uwa-da-wabi na ‘Yan bindigar, daga bisani kwale-kwalen ya kife a cikin  kogi.

A cewar wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ‘yan bindigar sun yiwa kauyen kawanya ne da karfe 1:00 na rana a Lahadin da ta gabata.

A Karanta Wanna:Rungumar Sana’a Ce Mafita Ga Matasa, In Ji Pharm. Sule

“Mun ga ‘yan bindigar suna tafiya kauyen Kalli a kan babura dauke da manyan  makamai domin kai wa al’ummar hari, lamarin da ya tilasta wa mutanen kauyen tserewa domin tsira da rayukansu.

A cewarsa, kwale-kwalen ya kife ne a kogin Birnin Magaji, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 20.

Ya bayyana cewa an gano gawarwaki biyar a kogin Falale, hudu a kogin Birnin Magaji, yayin da uku kuma aka gano su a kogin gadar Gummi.

Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun addabi al’umomin Kwammaka, Kwammaka Jibi, Kwammaka Mai Katsina, Kallin da Kazura, duk a karamar hukumar Gummi.

A Karanta Wanna:Gwamnatin Kano Ta Sassauta Dokar Hana Zirga-Zirga

Idan za a iya tunawa wanna ba farau bane a yankin Arewa maso yamma da Arewa maso gabas, a inda ‘yan bindiga kan yanka kudin fansa domin samun damar gudanar da aikin gona kokuma a matsayin haraji ga al’umma. A sau da dama kin biyan wanna bukatar, mazauna yankin kan hadu da ajalinsu.

Majiyar ta ce an yi kokarin jin ta bakin jami’an tsaro, amma basu ce komai ba. (DIMOKURADIYYA).

← Back

Thank you for your response. ✨

 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...