Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

An Haramta Fina-fina Da Suke Kwaikwayen Ta’addanci Da Daudu A Kano

EL Mustapha
EL Mustapha

Daga Abdullahi Sani Sulaiman

Sakamakon korafe-korafen al’umma a kan shirya fina-finan dake nuna faɗan Ta’addanci da harkar Daudanci a jihar Kano. Shugaban Hukumar tace fina-finai da Ɗab’i ta jiha Abba El-mustapha ya bada umarnin dakatarwa tare da hana dukkan fina-finan dake nuna faɗan Daba da satar mutane domin neman kuɗin fansa da harkar Ƴan Daudu da makamantan su a faɗin jihar Kano.

Abba El-mustapha ya bada wannan umarni ne jim kaɗan bayan wata ganawa da yayi da manyan ma’aikatan hukumar ta tace fina-finan tare da wasu daga cikin wakilan yan masana’antar shirya fina-finan ta kannywood wanda suka haɗa da Ƙungiyoyin MOPPAN, AREWA FILMS MAKERS, Masu bada umarni (DIRECTORS) da kuma masu shirya fina-finai (PRODUCERS).

A Karanta Wanna:Faɗan Daba Da Kilisar Dawaki Zasu Zamanto Tarihi A Ƙaramar Hukumar Birni – Inji Chilla
Abba ya kara da cewa doka ce ta bawa hukumar damar dakatarwa ko hana duk wani film da yaci karo da tarbiya tare da al’adar al’ummar dake jihar Kano, a saboda haka tuni lokaci ya shige da za’a zuba ido irin wannan gurbatattun fina-finai su cigaba da yaɗuwa a cikin al’umma.

El-Mustafa ya bawa masu shirya irin waɗanan fina-finan damar wata ɗaya da su gyara aiyukan su kafin doka ta fara aiki gadan-gadan a kan su.

Shugaban ya gode wa yan masana’antar shirya fina-finan ta kannywood dangane da haɗin kai da kuma goyan bayan da suke bawa hukumar a ko da yaushe.

A Karanta Wanna: Zargin Almundahan: Gwamnatin Kano ta Gurfanar Da Ganduje da Matarsa da Wasu Mutane 6 A Kotu

Ya kuma godewa al’ummar jihar Kano kan irin haɗin kan da suke bawa hukumar musamman na sanar da ita duk wani abu da suke ganin ya saɓawa al’ada da tarbiyar da kuma addinin musulunci.

← Back

Thank you for your response. ✨

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...