Daga Abdu Ado
Shugaban riko na Ƙaramar Hukumar Biirnin Kano , Hon, Bashir Baba Chilla ya ce faɗan daba da klisar dawaki ba bisa ƙa’ida ba zasu zamanto tarihi a cikin birni bisa kyakyawan shiri da suke da jami’an tsaro domin fitar da alkibila mai ɗorewa.
Read also: Mazauna Kusa Da Madatsar Ruwa ta Ghari Da Su Yi Nesa Da Kogi – Inji Shugaban Ƙaramar Hukuma
Bashir Chilla shi ya bayyana hakan a zantawar sa da manema labarai a ofishinsa.
Ya ce nan bada jimawa ba zasu kawo ƙarshan masu fadan daba da Kuma masu yin kilisar Dawaki, a cikin Ƙaramar Hukumar Birni, domin rage hasarar rai da dukiyar al’ummar da basu-ji-basu gani ba.
Read also: Ƙaramar Ministar Abuja, Dr. Mariya Bunkure ta Faranta Zukatan Tsofaffin Abokan Aikinta Na AKTH
“Wannan matsala ta daɗe tana ciwa mutanan ƙaramar hukumar birni tuwo a ƙwarya inda ake samun hasarar rayuka sakamakon kilisar Dawaki da kuma uwa uba ta’addacin matasa masu faɗan daba a dukkanin saƙo da lunguna ƙaramar hukmar.
Ya ce daga shigar su ofis sun sami damar zama da shugabannin ƙungiyoyin masu hawan kilisar dawaki don lalubo bakin zaran don magance matsalar duba da yanayin bukukuwan Sallah dake ƙaratowa.
Read also: Masu Zanga-zanga sun ƙone Fadar Sarki da ofishin hukumar NDLEA ƙurmus a jihar Kwara
Baya ga haka Kuma tuni “muka tattauna da jami’an tsaro ta yarda zasu bada cikaken tsaro tafannoni da dama musamman akan abin da ya shafi harkar daba da shaye shaye”. Inji Chilla.
Ya kara da cewa zasu yi iya yinsu wajan bada goyon baya don samun nasara tare da tabbatar da samun zaman lafiya a ƙaramar hukumar da jiha baki ɗaya.



























