Karshen Tukatuki Tuk: Kwamishina Sufuri Namadi Ya Ajiye Aiki Sakamakon Badaƙalar Belin Mai Sayar Da Kwaya
Daga Sunusi K/Na’isa
Read also: ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Bayan Gwamnatin Tarayya Ta Biya Buƙatar Su
Kwamishina Sufuri na jihar Kano Alhaji Ibrahim Namadi ya ce ya ajiye aikinsa na Kwamishina da Gwamna Kano Abba Kabir Yusuf ya ba shi don kashin kansa.
Belin Dan Safarar Kwaya: Gwamna Abba Ya Umurci A Gaggauta Bincikar Zargin Hannun Kwamishinan Sufuri
Tsohon Kwamishina ya sanar da haka a wani fefan bidiyo da ya saki na kimanin minti 3:42 jim kalan da Gwamna Kano Abba Yusuf ya karbi rahoton binciken badaƙalar belin gawurttaccen mai Safarar miyagun ƙwayoyi a jihar, Sulaiman Danwawu Fagge.
Read also: Wazirin Ningi Ya Yi Murabus, Sakamakon Tsoma Siyasa a Harkokin Masarautar Ningi
Yaɗuwar Sankarar Mama: Mata 500 Sun Kamu a Kwana 210 – TMP. Adamu Yusuf
Namadi ya ce duk da abin da yayi bai sabawa dokar ƙasa ba domin kuwa mai Shari’a shi ya bashi damar karɓar belin. Amma hakan bai kyautu a gareshi ba domin ya kare mutunci da daraja ta jihar Kano da kuma gwamnati. Tsohon Kwamishina ya godewa gwamnati tare da bada tabbacin ci gaba da tallafawa wa gwamnatin Abba Yusuf a kokarinta na fafutikar yaƙi da miyagun kwayoyi.




























