Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Iran Ta Saki Makamai masu Linzamin 150 a Safiyar yau Asabar Akan Ƙasar Israel 

Iran
Iran

Iran Ta Saki Makamai masu Linzamin 150 a Safiyar yau Asabar Akan Ƙasar Israel

Daga Adita

A ƙoƙarin ramuwar gayya sakamakon kutse da hare-haren da ƙasar Israel ta kai mata na wanda yai sanadiyar kashe wasu jigajigan Kwamandojinta , Iran ta sake  Ƙaddamar da sabon hari da makamai masu Linzami 150 a wani farmaki wanda tai wa laƙabi da  sunan “Honest Promise 3”.

A safiyar yau Asabar, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta ƙaddamar da  sabon harin da makamai masu linzami a kan Isra’ila, wanda ta sanya wa suna “Honest Promise 3”.

Wannan harin ya biyo bayan hare-haren da Isra’ila ta kai a baya wanda ya yi sanadin mutuwar wasu manyan hafsoshin sojin Iran da fararen hula da yawa a wasu sassan yankin Gabas ta Tsakiya.

A Iya Karanta Wanna:Iftula’i: Barayin Waya Sun Kashe Wani Haziƙin Ma’aikacin Jami’ar Northwest a Kano

Rahotanni daga kafofin yaɗa labarai na Cikin gida Iran, kamar Almayadeen Al-arabiya sun bayyana cewa harin ya ƙunshi jefa manyan makamai masu linzami da kuma wasu jiragen yaƙi marasa matuƙa (drones) zuwa yankunan Isra’ila, da nufin ɗaukar fansa kan abin da Iran ta kira “kisan kai ba tare da wani dalili ba da Isra’ilan ta aikata a kanta.”

Tuni Ma’aikatar tsaron ƙasar Iran ta ce wannan harin wani bangare ne na jerin martanin diflomasiyya na soji da ƙasar ke ɗauka don kare martabarta da tsaron iyakokinta da kuma al’ummarta. Wannan shi ne karo na uku cikin jerin hare-haren da Iran ke daukar nauyin su, wadanda aka sanya wa suna “Honest Promise”, domin mayar da martani ga ƙasar ta Israel tare da nuna mata cewar Iran ta shirya domin gwabza yaƙin.

Iran ta ce hare-haren da Israel ta kamata ya shafi sojojinta da farar hula da kuma abokan ƙawance ta wanda ta lashi takobin ɗaukar fansa.

A Iya Karanta Wanna:Hafsan Sojoji Burtai Ya Kai da Kyar Sakamakon Harin ‘Yan Boko Haram A Borno

Yaƙin da mahalkanta ke hangen idan shugabannin duniya ba suyi da gaske ba, to tabbas ka iya zama yaƙin duniya na uku kuma idan ya zamanto hakan Allah ne yasan yawan asarar da za ayi wanda ya shafi rai da ɗinbin dukiya, wanda hakan ka iya kawo rushewar wasu ƙasashe musamman ta fuskar tattalin arziki.

 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...