Daga Sunusi K/Na’isa
Kungiyar tarayyar turai (EU), da ƙasar Jamus sun ƙaddamar da kaso na 3 na shirin tallafawa Najeriya dangane da abinda ya shafi makamashi wato NESP domin habbaka sabbin dabarun hanyoyin samar da isashshen makamashi musamman a yankunan karkara.
Read also: JAMB ta Dakatar Da Karatun Digirin Haɗaka Tsakanin Jam’i’o’i da Kwalejojin Ilimi A Najeriya
An yi ƙiyasin shirin zai laƙume kuɗin da ya kusa yuro miliyan 18 a inda za a sada mutane 1,500 da lantarki da kuma samawa mutane dubu 30 gas na girki.
A Iya Karanta Wanna:Kwan- Gaba Kwan-Baya: Arewa Baza Ta fita Daga Duhu Ba Sai Nan Da Sati 2 – Inji Minista
Haka zalika a kashin na uku na wannan shirin za a samar da wutar lantarki mai ƙarfin Megawatts 8.
Read also: Chanza Takardar Naira Zai Kawo Ƙarshen Rike Kuɗi a Hannun Yan ta’adda a Najeriya -Ado Dansudu
Tallafin na samar da makamashi ga Najeriya an fara ƙaddamar da shi tun a shekarar 2013 wanda kungiyar tarayyar turai EU da tallafin ƙasar Jamus haɗin gwiwa da ma’aikatar lantarki ta Najeiya.
Read also: Shugaban Burkina Faso ya kori Jami’ar Majalisar Dinkin Duniya Carol daga ƙasar
Kungiyar ta tarayyar turai ta amince ta ƙara zuba kuɗi a kashi na 3 na wannan shiri domin taimakawa ci gaban da kuma samar da tsarin lantarki ta sabbin hanyoyin makamashi da kuma tabbatar da jama’a sun amafana da shirin.
Mataimakin Ambasadan ƙasar Jamus Johannes Lenhre ya tabbatar da shirin ƙasarsa wurin cimma muradan da Najeriya ta sanaya a gaba a fannin makamashi.
A Iya Karanta Wanna:Rigakafin Shan-Inna: Dakta Labaran ya Yabi Ƙananan Hukumomin Uku
Sakataran ma’aikatar lantarki na Najeriya Mahmuda Mamman ya yaba da irin tallafin da Najeriya ke samu daga kungiyar tarayyar turai da Jamus musamman yadda suke ƙoƙarin tabbatar da samun isashshen makamashi a ƙasar.




























