Farasesa Ibrahim Maibushira Ya Zama Shugaban Kungiyar Safinatul—-
An nada shahararren masanin fanin ilimin addini Musulunci na Jami’ar Bayero ta Kano, Farafesa Ibrahim Mu’azzam Maibushira a matsayin sabon shugaban kungiyar Safinatul Khair dake jihar Kano.
Read also: Rigimar Masarautar Kano Na Daf Da Zama Tarihi, In Ji Kwamishina Waiya
Nadin ya biyu bayan sakamakon taron mitin na musamman da dukkanin shugabannin sassa na Kungiyar Safinatul- Khair suka gudanar a ofishin kungiyar dake unguwar Diso, a inda taron ya amince da Farafesa Ibrahim Mu’azzam Maibushira ya zama cikakken shugaban kungiyar Safinatul khair a karo na uku da kafuwarta.
A Karanta wanna:Hukumar Yaki da Ta’ammali da Miyagun Kwayoyi da Kwacan Waya: Tayi Holin Wasu Matasa Ga ‘Yanjaridu A Kano
Taron na gaggawa ya gudana ne a ofishin kungiya a ranar Alhamis, wacce tai dai-dai da cikar kwana bakwai da rasuwar tsohon shugaba kungiyar Malam Ahmad Garba Amin Kofarnaisa wanda ya riga mu gidan gaskiya.
Read also: Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
Idan za a tuna, Malam Ahmad Garba ya riƙe wanna kungiya har tsawon shekaru 28 wato bayan kafuwarta da shekara daya. Wanda a karkashin jagorancin sa kungiyar tai shura tare da samun gagarumin nasarori da ci gaba mai tarin yawa, hakan ya sa tazama tauraruwa tsakanin takwarorinta da ke fadin jihar Kano.
Malam Ahmad ya rasu ranar 5 ga watan Satumba bayan ya sha fama da jinya. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya karbi ayyukan Malam ya kuma shafe kurakuransa.
A Karanta Wanna:‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Asibitin Kaduna Tare da Sace Ma’aikatan Jinya
Game da Sabon shugaban kungiyar ta Safina, Malam Ibrahim Maibushira shi ya fara jagorancin kungiyar a matsayin na riko a lokacin da aka kafata, shekaru 29 da suka gabata. Haka kuma Farafesa Maibushira na daga cikin waɗanda suka hassasa samuwar Hisbah a jihar Kano wanda kuma har ya zama Babban Kwamanda a hukumar.
Read also: Jami’in KAROTA Yayi Sanadin Kama Wani Da Ake Zargin Barawan Mota da Kuma Kungiyar Su A Kano
Malam Ibrahim ya zama Babban Darakta a Hukumar bayar da Zakka da Hubisi ta jiha baya ga mukamai daban-daban da ya rike a fannonin ilimi da jagoranci a gurare da dama, muna addu’ar Allah yai masa jagoranci.
Kungiyar Safinatul-Khair Foundation, kungiya ce ta halin kan unguwannin, Lokon makera da Sagagi, da Gwale da Diso. An samar da ita bisa turakun samar da ilimi da sana’a da kuma kyautatuwar tarbiyya ta matasa yankin da ma jihar Kano baki daya.




























