Alamu sa Nuna Kamfanin NNPCL Ya Kara Kuɗi Man Fetur Zuwa ₦897 ….
A bisa kyakkyawan alamu Kamfanin mai na Najeriya, NNPCL ya ƙara farashin sayar da mai daga ₦617 zuwa ₦897.
Alamu sun nuna hakan bayan da aka wayi gari da dogayen layi a gidajen mai a kusan dukkan manyan jihohi a ƙasar Najeriya.
Read also: Hukumar Kamfanin Fortune Rice Ta Musanta Labarin Rufe Kamfanin Bisa Zargin Karya Dokar Muhalli
A Karanta Wanna:Ƙasurgumin Dan Dabar Da Ya Addabi Jama’a A Kano Burakita Ya Sheka Barzahu
Read also: Rashin Kulawa Na Daga Cikin Bukatun Da Matar Gwamna Abba Ta Kai Kara A Kotu Don A Raba Su
Tuni dai wasu gidajen man fetur a Najeriya suka sauya farashin litar zuwa sabon farashin duk da har ya zuwa haɗa wanna rahoton bamu sami cikakkiyar sanarwa karin farashin man fetur ɗin ba daga hukumar ta NNPCL ba.
Wannan dai na zuwa ne kwana ɗaya bayan da kamfanin na NNPCL ya bayyana cewa yana fuskantar matsalar ƙamfar kuɗi, wani abu da ya sa ƴan Najeriya ke hasashen kamfanin na koƙarin sanar da sabon farashin, amma daga bisani hukumar ta barranta kanta da karin kudi farshin man.
Read also: NASIR EL-RUFAI YA NEMI AFUWA KAN KARAR DA ICPC TA SHIGAR A KANSA
A Karanta Wanna:Shugaba Tinubu Ya Umarci Kamfanin NNPCL Ya Biya Tallafin Man Fetur
Tun dai bayan da gwamnatin shugaba Tinubu ta sanar da janye tallafin man fetur a jawabinsa na ranar 29 ga watan Mayun 2023, ƴan Najeriya ke fuskantar sauye-sauye a farashin man wanda kuma ke taɓa sauran sassan rayuwa waɗanda suka jawo matsananciyar tsadar rayuwa a ƙasar.



























