Daga Wakilinmu
Shugaban kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi, Alhaji Abdul Bashir Husaini ya ce daga yanzu sun hana kasa kaya a baro ko kura a hanya domin kawar da cinkoso a cikin kasuwa.
Read also: An Gargadi Ƴan Jaridar Yanar Gizo Da Suyi Aiki da Kwarewa Tare da Ƙare Martabar Kasa
Alhaji Abdul Bashir ya sanar da haka da yake zantawa da manema labarai, inda yace suna so su tsaftace kasuwar a sakamakon cunkoson da ya dabaibaye kasuwar, kusan shekara uku da suka gabata.
Read also: NBA Ta Bukaci a Dakatar da Dokar Gyaran Haraji Saboda Kuskurewa Bin Tsarin Doka
Ya ƙara da cewa Hukumar kasuwar sun zauna da ƙungiyoyin dake cikin kasuwar domin a sami kyakkyawan yanayi don magance matsalar da take kawo cunkoso a kasuwar.
Read also: Rashin Kulawa Na Daga Cikin Bukatun Da Matar Gwamna Abba Ta Kai Kara A Kotu Don A Raba Su
” Yace ba zai yiwu ba adinga ɗebo kaya daga cikin shago kuma a kasa su a kura ko baro ba, yin hakan an shiga haƙin hanya da masu saye da siyarwa.
Ya kamata masu wannan ɗabi’a su gane ba anyi ne don a muzguna musu ba ko a hanasu kasuwanci ba, sai dai domin a kawo gyara domin ci gaban kasuwar da kasuwanci a jihar Kano bak ɗaya” . Inji Bashir.
Shugaban ya ce, hukumar kasuwa ta yarda ƴan kasuwar zasu iya kasuwancin su a hannu ko a kwali, inda yace yin hakan bai saɓawa doka ba. Amma kasa kaya a cikin kura ko baro wannan bazamu taɓa lamunta ba ko kaɗan. inji Abdul Bashir.



























