Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

DA ƊUMIN SA: Kotu Ta Yanke Hukunci Rataya Ga Ɗan China Saboda Kashe Masoyiyarsa A Kano

Frank
Frank

Daga Wakilinmu

Babbar kotun jihar Kano ta yanke wa ɗan kasar China Frank Geng Quarong hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon samunsa da laifin kashe mai masoyiyarsa, Ummulkhulsum Sani Buhari.

Idan za a tuna, Quarong ya daɓa wa Buhari wuƙa ne a lokacin wata taƙaddama kimanin watanni 7 da suka gabata a gidansu.

Lamarin ya faru ne a ranar 16 ga watan Satumbar 2022. Domin tabbatar da laifin, mai gabatar da ƙara ya gabatar da shaidu shida, da suka haɗa da mahaifiyar wanda aka kashe, da ‘yar uwa, da wani maƙwabcinsu, da jami’an ‘yan sanda daga Ɗorayi Babba da kuma sashen binciken manyan laifuka na jihar da ke Bompai a Kano. Quong ya bayar da shaida wajen kare kansa.

Da yake yanke hukuncin a ranar Talata, Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji ya gano mai gabatar da ƙara ya tabbatar da laifin batare da wani shakku ba. A karshe ya ce bisa ganganci Quong ya kashe Buhari ta hanyar shiga gidan ta ba tare da gayyata ba sannan ya yi watsi da iƙirarin kare kan sa.

Kamar yadda sashi na 221 na dokar (Penal Code Law) ya tanada, an yanke wa Quong hukuncin kisa ta hanyar rataya. Mai shari’a Ma’aji ya kuma bayar da shawarar cewa, kwamitin da ke kula da ayyukan jinkai ya sake duba shari’ar, kamar yadda sashi na 113 na dokar gudanar da shari’ar manyan laifuka, Kano 2019 ya bayar.

Babban lauyan gwamnatin jihar Kano, Barista Haruna Isa Dederi, ya yaba da hukuncin tare da bayyanashi a matsayin wata muhimmiyar ci gaba a tarihin shari’a. Lauyan da ke kare mai laifin Barista Muhammad Dan’zumi ya ce suna da niyyar daukaka ƙara kan hukuncin a kotun daukaka ƙara.

Tsohon Babban Lauyan Tarayya kuma Kwamishinan Shari’a, Musa Abdullahi Lawan ne ya fara gabatar da ƙarar a ƙarƙashin sa-idon Babban Lauyan Jihar Kano na yanzu, Barista Haruna Isa Dederi.

← Back

Thank you for your response. ✨

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...