Daga Wakilinmu
Kimani kwanaki huɗu ke nan mutanan Ɗiso da Lokon maƙera suka haɗu da iftila’i wanda ɓarayi suka sace wayoyi a injin bada wutar lantarki ta kwanar Ɗiso.
Read also: Iftila’i: Yara Biyu Sun Mutu Sakamakon Mamakon Ruwan Sama
Shugaban Kwamitin da ke lura da injin bada wutar lantarki wato transifoma, Alhaji Ibrahim Garba Aminu Ƙofarnaisa shi ya sanar da haka da yake zantawa da manema labarai.
Ibrahim Ƙofar naisa, ya danganta rashin samun tsayayir wutar lantaraki ita ta bawa ɓarayin damar sace muhimman wayoyi a jikin injin wutar na manƙudan kuɗaɗe. Don haka ya yi kira ga masu hannu da shuni da shugabanin masu riƙe da madafin iko da ƴan siyasa da su kawo ɗauki ga al’ummar yankin.
Ya ce kwamitin ya tuntuɓi hukumar KEDCO amma shugabanin sun ce babu abin da za su iya, sai dai jama’ar ungwar su sama wa kansu mafita.
Read also: Chanza Takardar Naira Zai Kawo Ƙarshen Rike Kuɗi a Hannun Yan ta’adda a Najeriya -Ado Dansudu
Don haka yana roƙon wakilin Ƙaramar hukumar na Gwale a Majalisar tarayya, Alhaji Garba Ɗiso da na majalisar Dokoki na jiha Hon. Abdulmajid Isah Mai rigar fata da sauran masu hannu da shuni na yankin da su taimaka wajen tabbatar da gyaran inji bada wutar lantarkin ganin gabatowar azumi ga kuma matsanancin zafi.
Alhaji Ibrahim Garba ya roƙi jami’en tsaro da ƴan hisbah da su kawo wa jama’ar kano ɗauki na yaƙi da masu satar kayyan injin bada wutar lantarki cikin gaggawa. ya ce ya zuwa wanna lokai rahotani sun tabbatar da an saci kayyan transifoma 17 a cikin birni da kewaye.
A halin yanzu kimani kwana huɗu ke nan da aikata wannan tabargaza na sace waɗanan muhimman wayoyi a injin bada wutar lantarkin a unguwar Ɗiso, wanda kimani kaso 85 na mutanan unguwar Ɗiso da Lokon maƙera da Sagagi da Gwale sun dogara kacokan da ruwan burtsatse kuma ruwan yana samuwa ne kawai ta samuwar wutar lantarki.
Read also: Fiye da Musulmi Miliyan Uku Sun Hallara a Katsina don Mauludin Sheikh Ibrahim Niasse
Wasu ƴan asalin unguwar, Abubakar Sa’id da Sadiq Diso sun ce mafi yawa daga al’umar unguwani Ɗiso da Lokon maƙera sun nuna damuwarsu da yanayin da suka shiga na duhun-duhununu, ga matsanacin zafi ga azumi za a shiga ga uwa-uba rashin samun ruwan sha wanda dama daga rijiyoyin burtsatse ake samu.
Sun ce a halin yanzu da akwai barazanar ɓarkewar cuttuka sakamakon rashen wadattace kuma tsaftattacen ruwa sha a ƴankin. Don haka suke roƙon masu farcen susa da ƴan siyasu da suke wakiltar yankin da su bada tallafi na gyara injin wutar lantarkin.




























