Daga Wakilinmu
Mai Martaba Sarkin Rano Ambasada Kabiru Muhammad Inuwa, ya bada umarnin faɗaɗa bincike tun bayan gano wata bindiga kirar AK-47 a cikin kogin Ruwan garin Taɓo dake yankin ƙaramar hukumar Tudun-wada.
Sarkin ya bayar da umarni ne bayan karɓar rahoton da wakilin Mai Martaba Sarki a ƙaramar hukumar Tudun-wada Alhaji Bako Alu ya gabatar ga Sarki na ganin bindigar a kogin ruwan Garin Taɓo a zaman fadar sarki a ranar litinin.
Kamar yadda jami’in yaɗa Labarai na masarautar Rano Nasiru Habu Faragai, ya shaida mana, ya ce wani mai sana’ar kamun kifi ne mai suna Yakubu Umar Kurma ranar laraba 21/02/24 da misalin karfe shida na yamma ya tsinci bindigar a lokacin da yake sana’ar su, wato kamun kifi a cikin ruwa.
A karanta wannan: Ana Zargin Almajiri Mai Shekaru 17 Ya Hallaka Kansa Ta Hanyar Rataya A Garin Tudun-Wada
Read also: Iftila’i: Yara Biyu Sun Mutu Sakamakon Mamakon Ruwan Sama
Ganin hakan ke da wuya abinka da sai ya yi ta kwaroroto har sai da sauran jama’a dake kusa da shi suka ankara kuma da fahimmatar abin da yake ƙoƙarin nusar dasu kana suka garzaya domin sanar da Mai unguwa zuwa Dagaci zuwa wakilin Mai Martaba Sarki zuwa ‘Yan sanda da kuma mai riƙon shugabancin karamar hukumar Tudun- wada.
Wakilinmu, ya tattauna da wakilin Sarkin Rano a ƙaramar hukumar Tudun-wada Alhaji Bako Alu kan wannan lamari.
Wakilin Sarkin ya ce. ” Na gabatarwa Mai Martaba Sarki kan yadda wannan labari ya faru tare kuma da shaidawa baturen ƴan sanda na ƙaramar hukumar Tudun- wada da kuma shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Tudun-wada na yadda wannan lamari ya faru”.
A karanta wannan: YUNWA TA SA LEBURORI HAKAR GIDAN TURURUWA A BAUCHI
Read also: “Babu Wani Dalilin da Zai Sa Na Yi APC”, Wanna Wasan Fulani Ne da Kanuri – Sule Lamido
Alhaji Bako Alu ya kuma ƙara ce a halin yanzu sun miƙa bindigar AK-47 ga Baturen ‘yan sanda na ƙaramar hukumar Tudun-wada domin faɗaɗa bincike, kamar yadda Sarki ya bada umarni.
Haka kuma a yayin zaman fadar, Sarkin Rano Ambasada Kabiru Muhammad Inuwa ya yi kira ga al’ummar masarautar ta Rano dasu ci gaba da bawa jami’an tsaro haɗin Kan da ya kamata ta hanyar basu rahotannin siri domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.




























