Daga wakilinmu
Kafar yaɗa labarai ta STENTORNEWS ta samu rahoto daga jami’in yaɗa labarai na shiyyar Rano, Nasiru Habu Faragai, wanda ya yi bayani a kan zaman fadar sarkin Rano. Ya bayyana cewa Idris Nasiru ɗan shekaru goma sha bakwai da haihuwa Almajiri ne ya kawo karshen rayuwarsa da kansa ta hanyar rataya a garin Tudun Wada, ƙaramar hukumar Tudun Wada.
Read also: Motar Dangote Ta Kashe Mace Mai Ciki, Yaro Da Mutum Shida A Ondo
Wannan sanarwa ta fito ne ta hanyar wani rahoto da aka karanta a gaban Sarkin Rano, Ambasada Kabiru Muhammad Inuwa, a fadarsa. Rahoton wanda ya fito daga ofishin Wakilin Sarkin Rano da ke ƙaramar hukumar Tudun Wada, Alhaji Bako Alu, ya ambaci cewa an gano Idris Nasiru ne a rataye, kuma ƙoƙarin da ake yi na gano dalilin faruwar lamarin ya ci tura.
Rahoton ya bayyana cewa, “A ranar Litinin, 22/1/2024, Idris Nasiru ya je wani gini da ba a kammala ba a garin Tudun Wada, ya yi amfani da ‘buhun ɓuntun shinkafa’, ya hau, ya kuma rataye kansa. Daga bisani malaminsa Malam Ayuba Sha’aibu ya bi sahunsa ya same shi ya rasu.”
Read also: Matashi Mai Shekara 24 Ya Kashe Mahaifinsa A Bauchi
“Bayan gano Idris Nasiru a cikin ginin da ba a kammala ba, malamin ya kai rahoto ga Dagacin Tudun Wada da rundunar “ƴan sandan ƙaramar hukumar,” rahoton ya ci gaba da cewa.
Daga nan ne aka kai Idris Nasiru babban asibitin Tudun Wada domin tabbatar da lafiyar shi, amma rahoton wani likita ya tabbatar da mutuwarsa.
A cewar rahotannin, wani abokin Idris, wanda shi ma Almajiri ne mai suna Nura, ɗan shekara goma sha bakwai da haihuwa, da farko ƴan sanda sun kama shi ne saboda shakkun da suke da shi na yin fito-na-fito kafin Idris ya bace. Sai dai an sasanta da su, kuma yanzu haka rundunar ƴan sandan Tudun Wada na tsare da Nura domin ci gaba da yi masa tambayoyi.
Bayan jin rahoton, Sarki Ambasada Kabiru Muhammad Inuwa ya bayar da umarnin tura shi ofishin ƴan sanda na Rano domin sake gudanar da cikakken bincike kan lamarin.”
SENTORNEWS ta yi ƙoƙarin jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan Najeriya a shelkwatar Kano ta wayar tarho, amma ƙoƙarin bai yi nasara ba. Mun aika da sako a ƙoƙarin haɗa rahoton, amma ba mu samu amsa ba.





























Pingback: "A Binciki Yadda Aka Sami Bindiga AK-47 A Kogin Ruwan Garin Taɓo," Inji Sarkin Rano - The StentorNews Hausa