Daga Muazu Hardawa
Leburori da dama ƴan rabbana ka Wadata mu, masu aikin karfi a Bauchi sun koma tona gidan tururuwa don neman abin da za su ci, saboda matsalar tsadar rayuwa da rashin samun abin sawa a bakin salti, tun daga lokacin da aka janye tallafin man fetur a Najeriya.
Read also: Za a Fara Jigilar Alhazan Jihar Bauchi Daga Ranar 7 Ga Watan Mayu
Abubakar Salisu Nagiyaɗe, magidanci ne, wakilinmu ya ci karo da shi a Ibrahim Bako Byepass a safiyar wannan rana ta litinin inda ya haɗa zufa yana haƙar gidan tururuwa don neman shinkafar da tururuwar suka tara.

Abubakar
Nagiyaɗe, Ya ce akwai Ramin da ya samu kusan mudu biyu a wannan rana kuma ya koma kan sabon rami Wanda idan ya dace zai iya haɗa mudu biyar idan aka gyara za a iya samun mudu biyu na shinkafar tuwo wanda ya kai naira 3400.
Abubakar ya ce a leburancin wuni guda basa wuce dubu biyu ko uku Shima babu aikin. “Gyaran masai ne idan aka samu ake aikin dubu biyar zuwa goma shima ba mutum guda ba, kuma a halin yanzu samun aikin yayi wuya”. Abubakar ya faɗa.
Read also: Matashi Mai Shekara 24 Ya Kashe Mahaifinsa A Bauchi
Ya ce yana da mata ɗaya da yara 8 dole ya fara aikin tone ramin tururuwa don samun abin da zasu ci. ” Ta wannan hanya kawai zan samu mafita, na fahimci wani lokacin an fi samun tsabar sai kuma a ji da cefane ko kuma nu bayar da shinkafar a ba ni masara don sai muyi cefane, da haka muke rayuwa.” Inji Abubakar.
Burkilan ya ƙara da faɗin a yanzu haka yana da ƴan mata huɗu waɗanda sun gama makarantar firamare da ƙaramar sakandare (JSS) amma rashi ya sa suna zaune da su a gida, ya ce sai ko Islamiyya tunda malaman ko naira ɗari aka ba su suna hakuri, bayan haka ga gidan haya da sufuri.
Game da tallafin gwamnati kuwa, Malam Abubakar, ya ce basu taɓa samun ko ƙwaya ba, kuma sune suke layi lokacin zaɓe da iyalan su amma ba abin da suke samu, duk wanda suka zaɓa sun gudu masu kuɗi kuma yawanci basa taimaka musu don haka sun bar komai a hannun Allah, inji Nagiyaɗe.
Read also: Gwamnan Bauchi Bala Mohammed Ya Ƙaddamar da Hasken Solar a Dajin Yankari





























Pingback: Sama Da Mutane 100 Suka Tagayyara Sakamakon Tashin Gobarar A Sansanin Ƴan Gudun Hijira Dake Bauchi - The StentorNews Hausa