Daga Wakilinmu
Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil ya ƙalubalanci bayyana cewa sadaki ya kai Naira dubu chasa’in. “Ba a yi amfani da ilimin addini ba wajen cewa yanzu mafi ƙaranci sadaki ya haura Naira dubu casa’in,” in ji Shehin malamin.
Read also: Chanza Takardar Naira Zai Kawo Ƙarshen Rike Kuɗi a Hannun Yan ta’adda a Najeriya -Ado Dansudu
Idan za a iya tunawa a makon da ya gabata wasu kafofin yaɗa labarai sun rawaito cewa fadar Sarkin Musulmi ta fitar da cewa mafi ƙaranci sadaki yanzu a Najeriya ya haura Naira dubu casa’in.
”Bai kamata a yi amfani da yadda ake canjin Dala ko tsadar kayan da ake fama da su a yanzu ba, saboda ƙirƙirarru ne, shi kuma Addinin Musulunci kullum sauƙi yake kawo wa mutane ba azabtar da su ba. Don haka, akwai kuskure a ce mafi ƙaranci sadaki ya haura Naira dubu casa’in”.
Read also: Fiye da Musulmi Miliyan Uku Sun Hallara a Katsina don Mauludin Sheikh Ibrahim Niasse
Malam Ibrahim Khalil ya bayyana hakan ne yayin wani karatu da aka saba sakawa a shafinsa na Facebook.
”Magana ta gaskiya wadda ta dace da hankali ita ce mafi ƙaranci sadaki yana nan a Naira dubu 20, amma idan mutum yana da hali zai iya ƙarawa zuwa abun da ya sauwaƙa. Don haka, ku yi watsi da batun Naira dubu casa’in a matsayin mafi ƙaranci sadaki”.
Read also: HUKUMAR ICPC TA GURFANAR DA LIKITAN NASIRU ELRUFAI A GABAN KOTU
Malam Ibrahim Khalil ya yi suka da kaukausar murya cikin fushi kan yadda aka fitar da wancan bayani na mafi ƙaranci sadaki, inda ya ce idan aka biye wa wancan batun to da yawa ba za su iya yin auren ba, saboda mawuyacin halin da tattalin arzikin al’umma suke ciki a yanzu.
Don haka ya ƙalubalanci duk wanda ya ba da waccar fatawar, tare da ƙara tabbatar da mafi ƙarancin sadaki a kan naira dubu 20 ne, kuma ya kafa hujjoji da Ayoyi da Hadisan Annabi Sallahu Alaihi Wasallam da kuma fatawoyin malamai masu tarin yawa.




























