Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta tabbatar da an buɗe asusunta bayyan umarnin da Kwamanda Hisbah Sheikh Aminuddeen Ibrahim Daurawa ya bayar na gaggauta bincike tare da neman ba’asin rufe asusun. Babban Daraktan hukumar Alhaji Abba Sa’id Sufi ya tuntubi ma’aikatar shari’a domin samun shawarwari akan lamarin, a ta bakin Darkan Wayar da kai na Hukumar Hisbah, Auwalu Ado Shshe da ya sanar a ranar Asabar.
Idan za a tuna, Babban Kwamandan Hisbah Sheikh Aminuddeen Ibrahim Daurawa ya yi hira da kafar yaɗa labarai ta TRT Hausa akan lamarin, daga bisani Bankin ya fahimci kuskuran da ya tafka na rashin rubutawa hukumar Hisbah cewar Kotu ta umarcesu ne da kwarya-kwaryar hana taba kudinta da bai gaza Naia Dubu Taɓanin ba (N800,000) ne, ba a rufe asusun Bankin gaba ɗaya ba.
Read also: Hukumar Kamfanin Fortune Rice Ta Musanta Labarin Rufe Kamfanin Bisa Zargin Karya Dokar Muhalli
Daga bisani Bankin sun buɗe asusun ba tare da ɓata lokaci ba, bayan sun fahimci kuskuransu kuma suka nemi afuwan hukumar Hisbar.
Read also: HUKUMAR ICPC TA GURFANAR DA LIKITAN NASIRU ELRUFAI A GABAN KOTU
Darkan Wayar da kai na Hukumar Hisbah, Auwalu Shshe, ya ce rufe asusun Bankin hukumar, ya faru ne biyo-bayan wani sumame da hukumar ta yi wa wasu otal dake unguwar Sabon Gari a ƙaramar hukumar Fagge a jihar nan a shekarar ta 2019 wanda hakan ya sa ƙungiyar masu Otal suka gurfanar da hukumar a gaban kotu.
Read also: Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
Auwalu Sheshe, ya ce ɗaukar matakin da ƙungiyar masu otel ɗin su ka yi, baya rasa nasaba da irin ayyukan da hukumar ta hisbah ta ke yi ba-dare-ba-rana na umarni da kyakkyawa aiki da hani da mummuna. ” Toh! ko ma menene hukumar ba zata yi sako-sako ko ta fasa gudanar da ayyukanta ba kamar yadda doka ta sahale mata ba, na tsaftace jihar kano ta yaƙi da balala”. Inji Daraktan.



























