Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya NSCDC ta kama wani mai suna Chinana Tali bisa zargin shi da safarar bil’adama, da kuma yunkurin sayar da ɗansa ɗan shekara shida a kan Naira miliyan 20 a Abuja.
Kwamandan Hukumar ta NSCDC na babban birnin tarayya Abuja, Olusola Odumosu ya tabbatar wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce an kama wanda ake zargin ne a wajen siyar da yaron bayan an kama shi daga Benue zuwa Abuja.
Read also: Fiye da Musulmi Miliyan Uku Sun Hallara a Katsina don Mauludin Sheikh Ibrahim Niasse
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa wanda ake zargin ya tabbatar wa da Hukumar NSCDC yayin da ake yi masa tambayoyi a hukumar cewa wanda aka kamashi da shi, Ushafa Tali mai shekara shida a duniya, ɗansa ne na cikinsa halak malak.
Tali, ya bayyana ya ƙara da faɗin, shi mahaifin ’ya’ya shida ne kuma ya yanke shawarar sayar da ɗaya daga cikin ‘ya’yan nasa ne domin kuɗin su taimaka masa wajen kula da sauran iyalan.
Read also: Karo na Biyu: Kimanin Kayan Abinci na Sama da Naira miliyan 42 aka Rabawa Kungiyoyi a jihar Kano
Saboda yana shan wahala, “kuma babu kuɗi, don haka ina bukatar in sami hanyar da zan kula da sauran yarana,” in ji Tali.
Kwamandan Hukumar NSCDC ya ce kama mahaifin da ke tare da dansa ya biyo bayan samun bayanan sirri da suka samu daga wasu masu kishin ƙasa, na cewar mahaifin na neman farashi mai kyau a kan yaron domin sayarwa.
kwamandan ya ce za su kammala bincike daga bisani kuma su gurfanar da mahaifin a gaban ƙudiya.




























