Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Gwamnatin Kano Ta Kafa Kotun Tafi-Da-Gidanka Ga Masu Shan Ƙwaya Da Ƙwacen Waya

Abba
Abba

Daga Waklinmu

Kwamitin yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya na Jihar Kano ya kafa kotun tafi-da-gidanka domin gaggauta hukunta masu sha da sayarwa gami da masu ƙwacen waya a jihar Kano.

Shugaban kwamitin, Birgediya Gambo Mai’Adua (mai ritaya) ya tabbatar da haka da yake zantawa da manema labarai.

ya gargaɗi masu aikata shan miyagun ƙwayoyi da ƙwacen waya da su gaggauta daina wa ko su gamu da fushin hukuma, domin gwamnatin jihar Kano ba za ta lamunci muggan ayyukansu ba.

“Kwamitin yana da kotun tafi-da-gidanka kuma yana da niyyar gyara ɗabi’un waɗanda suka daina da kuma mayar da su cikin al’umma,” in ji Mai Adu’a

A cewarsa, akwai abin damuwa a cikin wani rahoto na baya-bayan nan, da ke nuni da cewa a duk mutum shida a jihar nan ɗaya na shan miyagun ƙwayoyi, don haka gwamnatin jihar ta ƙaddamar da yaƙi da masu aikata waɗanan laifukan.
Ya bayyana cewa kwamitin yana aiki tare da sauran hukumomin da ke yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da sauran laifukan masu alaka da su, don ganin an shawo kan yawan shan miyagun ƙwayoyi a Jihar Kano.

“Yaƙi da wadannan matsalolin haƙƙi ne na kowa da kowa. Magance wannan barazanar tun yanzu shi ne abu mafi alheri gare mu da al’ummarmu,” in ji Mai’Adua.

Jami’in kuma ya yi nuni da cewa, kwamitin zai mayar da hankali wajen farfaɗowa da sauya tunani da kuma dawo da waɗanda abin ya shafa cikin al’umma bayan sun gyaru

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...