Gwamnatin jahar kano ta amince za ta baiwa ma’aikatan jahar kano dana kananan Hukumomi Naira Dubu Ashirin a matsayin tallafin rage radadin janye tallafin man fetur daga watan Disambar 2023 da ya gabata.
Shugaban kungiyar kwadago ta TUC reshen jahar kano Comrade Mubarak Buba Yarima ya bayyana haka a cikin wata sanarwa.
Read also: Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
Sanarwar mai dauke da sa hannun sakataren kungiyar Comrade Abdu Usman Yalo ta ce gwamnatin ta kuma amince za ta baiwa ‘yan fansho Naira Dubu goma sha biyar Kowanne daga watan Disambar.
Read also: Gwamnatin Kano Ta Naɗa Sheikh Bazzallah Nasir Kabara A Matsayin Shugaban Hukumar Tace Fina-finai
Sanarwa ta ce gwamnatin ta amince da hakan bayan an cimma matsaya a tattaunawar da aka yi tsakanin kungiyoyin ma’aikata da kwamitin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa karkashin jagorancin Comrade, Baffa Sani Gaya mai baiwa gwamna shawara akan harkokin ma’aikata akan al’amarin.
Kungiyar kwadagon ta TUC ta yabawa gwamnatin jahar kano da shugaban kwamitin da ‘yan kwamitin da kuma shugabannin kungiyoyin ma’aikata bisa kokarinsu wajen cimma yarjejeniyar.




























