Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Yan Sanda Sun Kama Wata Matar Aure Da Mutane Biyu Bisa Zargin Kisan Kai A Kano

Mutanan da ake zargi
Mutanan da ake zargi

Rundunar ‘yan sanda a Kano ta kama wata matar aure mai suna Hafsat Sirajo mai shekaru 24 bisa zargin kashe wani matashi mai suna Nafiu Hafizu da wuƙa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammad Usaini Gumel, ya gabatar da wanda ake zargin tare da wasu mutane biyu a gaban manema labarai a ranar Juma’a.

Gumel ya ce Hafsat, wata mazauniyar Unguwa Uku da ke ƙaramar hukumar Tarauni, ta amsa laifin kashe mamacin ta hanyar daɓa masa wuƙa.

Ya ce an kama mijinta, Dayyabu Abdullahi mai shekaru 38 da kuma mai gadinsu Malam Adam mai shekaru 65 bisa laifin taimakawa wajen ɓoye gawar don ɓoye laifin kisan kai.

Hafsat ta shaida wa manema labarai cewa direban da ke zaune tare da su ya yi ƙoƙarin hana ta kashe kanta inda ya ƙwace wuka a hannunta.

“Na ɗan yanke a hannuna sai ya ce in je in canza tufafina. Ina fitowa daga banɗaki na hango shi kwance sai na ɗauki wukar na daddaɓa masa,” inji ta.

Kwamishina ‘Yan sanda na jihar Kano Muhammad Gumel, ya ba da tabbacin gudanar da bincike tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

 

Alfijir labarai

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...