Daga Sunusi A. K/Na’isa
Al’umar Unguwanin Diso da Sagagi da Lokon Makera da Gwale da Galadanci da kewaye sun nuna gamsuwarsu bisa nada Alh. Bashir Idris Diso a matsayin Akawun Majalisar Dokokin jahar kano.
Read also: “Babu Wani Dalilin da Zai Sa Na Yi APC”, Wanna Wasan Fulani Ne da Kanuri – Sule Lamido
Shugaban kungiyar Safinatul Khair Malam Ahmad Garba Aminu Kofar Na’isa shi ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci tawagar dattawa da masu unguwani na yankin domin taya murna da kuma fatan alkhairi ga sabon Akawun Majalisar Dokokin na jihar Kano a ofishin sa.
Mallam Ahmad Kofar Na’isa ya ce sun ziyarci sabon Akawun Majalisar ne domin ba shi shawarwari nagari da kuma tunatas da shi bukatar gina abin alkhairi da gudanar da jagoranci nagari domin bunkasar jihar Kano da kasa baki daya.
Read also: Gwamnatin Kano Ta Yaba da Nadin Shugabannin Gidajen Rediyo Bisa Cancanta
Haka kuma shugaban na Safinatul Khair ya gabatar da addu’a ta musamman domin samun nasara a yayin gudanar da aikin sa da Kuma samun dawamaman zaman lafiya da kwanciyar hankali a jiha da kasa baki daya.
A jawabin sa, Akawun Majalisar Alhaji Bashir Idris Diso (Marafan Madakin Kano) wanda ya bayyana muhimmancin kungiyar ta Safinatul Khair a fagen bunkasa harkokin ilimi da addinin musulunci da jin kai, ya ba da tabbacin daukar shawarwarin shugabannin da kuma ba da gudummawa wajen cigaban yankin da jiha baki daya game da shugabanci abin misali.
Read also: “Na Fasa Auren Yar Guda”, In ji Mai Wushirya
Alhaji Bashir Diso, ya godewa shugabbani bisa ziyarar, wace ya bayyanata a matsayin a bar karfafa gwiwa da kuma ‘yan uwantaka.
Shugabannin kungiyar ta Safinatul Khair suna tare da Mai unguwar Diso Alhaji Tijjani Bello da manyan muta ne da kuma mambin Kungiyar.



























