Daga Abdu Ado
Jiragen sojin Najeriya sun yi lugudan wuta akan kasurgumin Dan ta’adda Ali Alhaji Alheri, da makarrabansa, da suka hadar da yaran Dogo Gide.
Read also: Sojoji Sun Daƙile Hari Yan Bindiga A Kano
Sojojin sama na Najeriya sun kashe kasurgumin dan bindiga, Ali Alhaji Alheri, wanda aka fi sani da Kachalla Ali Kawaje, wanda ya jagoranci sace dalibai mata na Jami’ar Tarayya ta Gusau (FUGUS) da ke Jihar Zamfara.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, cewa an kashe Kachalla Kawaje ne ranar Litinin a Jihar Neja.
Read also: DA ƊUMI-ƊUMI: Wasu Fusatattun matasa sun kashe DPO ‘Yan Sanda har lahira a Kano
Majiyar ta kuma bayyana cewa, a ranar 6 ga watan na Disamba, jiragen soji sun kai hari sansanin Ali Kachalla da Dogo Gide, inda sukai musu lugudan wuta wanda ake zaton shi ne yai sanadiyar kashe wasu daga gaggan ’yan ta’adda.
Rahotani sun tabbatar cewa wadanda aka kashe sun hada da Machika (kanin Dogo Gide, kwamanda a kungiyar Gide) da Dan Muhammadu, wani hatsabibin mai garkuwa da mutane a sansanin Dogo Gide.
Read also: Boko Haram: Zulum ya bayar da gudummawar N30m ga iyalan hafsan sojojin da aka kashe, Alari
Kasurguman ’yan bindigar uku tare da wasu da dama, an kashe su ne a lokacin da suke kokarin kai hari a Jihar Neja.
Majiya maikarfi ta rawaito cewa Dogo Gide da Ali Kachalla su suka addabi sassan jihohin Zamfara da Neja.




























Maikudi Marafa
December 12, 2023 at 1:49 pm
Hakan yayi kyau kwarai da gaske.