Gwamnatin Jihar Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Alhaji Abdullahi Musa a matsayin Shugaban Ma’aikata na jiha.
Babban Sakataren yada labaran gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa shi ya sanarwa da manema labarai nadin a yammacin nan.
Yace nadin na zuwa ne bayan da tsohon shugaban ma’aikatan jihar kano Usman Bala ya kammala aikin sa , Inda yayi ritaya daga aikin gwamnati tun a watan mayun shekara ta 2023, kamar yadda doka ta tanada .
Read also: Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
Sanarwar ta ce Alhaji Abdullahi Musa kwararen ma’aikacin gwamnati ne da yayi aiki a hukumomi da ma’aikatun gwamnatin jihar kano, kuma haifaffen karamar hukumar Kiru ne.
Read also: Hukumar Shari’a da Rundunar Yan sanda a Kano za su kawo karshen faɗan daba da kwacen waya
Sabon Shugaban Ma’aikatan gwamnatin jihar kano Abdullahi Musa ya taba zama Babban Sakatare a gidan gwamnatin jihar kano da majalisar zartarwa ta jihar da kuma ma’aikatar aiyuka na musamman da Ma’aikatar Kuda Da’ar Ma’aikata wato (SERVICOM) da sauransu.
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bukaci sabon shugaban ma’aikatan da ya gudanar da aikin sa cikin kwarewa da bin dokoki da ka’idojin aikin gwamnati.



























