Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Gwamnatin jihar Kano ta Amince a biya Ma’aikata 9,332 ba tare da Bata lokaci ba a Nubamba

Gov Abba

Bayan kammala tantance ma’aikatan gwamnati sama da 10,000 da Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta dauka aiki kafin shudewar wa’adinta, Gwamanan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya amince a ci gaba da biyan Ma’aikata 9,332 albashin su bayan kwashe watanni biyu ana tantancesu.

Dr. Abdullahi Bichi, Sakataren gwamnatin jihar Kano shi ya sanar da haka da yake ganawa da manema labarai a ranar Juma’ar nan.

Ya ce sakamakon amincewar Gwamna Abba Kabir Yusuf da rahoton kwamitin tantance ma’aikatan, ya yarda a dawo da biyan Ma’aikata na gaskiya kan manhajar biyan albashi ta jiha a wannan watan na Nubamba domin ci gaba da biyan su albashin su.

Sakataren Gwamnatin Jihar ta Kano, ya ce a baya an yi kuskure wajen daukar ma’aikatan sakamakon rashen tanadin su a kasafin kudi na wannan shekara da aka basu aikin, Wanda a cewarsa hakan ya samawa ka’idar aiki.

Dr. Bichi, ya ce “jama’a za su so sanin cewa daga cikin wadanda gwamnatin da ta gabata ta dauka aiki a bisa kuskure sun hadar da wata yarinya ‘yar shekara 13 wanda hakan ya saba wa ka’idojin daukar aikin gwamnati.”

“Sauran kusa-kuran sun hadar da wadanda ke aikin hidimar kasa (NYSC) da Kuma wadanda suka kammala karamar Sakandare da daliban manyan gaba da sakandare Kuma ba su kammala ba, yayin da wasu kuma aka sanya su bisa kuskure ta hanyar tura su zuwa mukaman da ba na aiki ba”, inji Dr. Bichi.

Idan za a iya tunawa dai gwamnatin Abba Kabir’ ta dakatar da biyan ma’aikatan da gwamnati Ganduje ta dauka su 12,566 albashi bisa zargin tafka kusa-kurai da aka gani a lokacin da aka dauke su aikin tsahon watanni biyar da suka gabata.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...