Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Ƙungiya ta Gargadi Majalisar Kano kan Rushe Sabbin Masarautu

Majalisar Kano
Majalisar Kano

Daga Wakilinmu

Wata ƙungiya mai suna Inuwar Masarautar Bichi da ke jihar Kano ta gargadi majalisar dokokin jihar kan batun yunƙurin rushe sabbin Masarautu hudu da ke jihar, yayin da ake zaman zullumi a wasu bangarori.

Ƙungiyar ta buƙaci majalisar ta yi taka tsan-tsan da wannan batu, a cikin wata wasika da ta aika wa Kakakin Majalisar mai taken: “Ƴunƙurin Soke Ko Rushe Sabbin Masarautun Kano, Muna Roƙon Ku Da A Yi Taka Tsan-Tsan Kuma A Dakatar Da Wannan Ƴunƙuri”, Kwafin takardar da aka ba wa manema labarai a Kano a ranar Litinin.

“A kwanan nan ne kafofin yaɗa labarai a Kano suka ba da rahoton ɓullar wasu gungun mutane da ba a san ko su waye ba, na iƙirarin sunansu ƙungiyar ‘Yan Dangwale Coalition For The Protection Of Democratic Rights Groups (COPDORG), suna neman majalisar dokoki mai albarka ta soke sabbin masarautu da aka ƙirƙiro tare da maido da masarautar Kano guda ɗaya tilo, kamar yada suka ambata.

Ka karanta wanna: DA ƊUMINSA: Har Yanzu Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Shine Kwamanda Hisbah A Kano, Inji Hukumar

A cewar kungiyar, idan aka amince da bukatar waccan ƙungiyar ta (COPDORG), na iya haifar da mummunan koma baya ga masarautar Bichi da ma ragowar masarautun da ke jihar Kano.

A roƙon da suka gabatar a rubuce wanda Sakataren Ƙungiyar, Alhaji Bello Gambo Bichi da sauran mutane aƙilai saba’in da bakwai (77) suka sanya wa hannu, sun jaddada mubaya’arsu ga masarautarsu ta Bichi da ma sauran masarautun gaba ɗaya, tare da kira ga majalisa da ta kaucewa duk wani yunƙuri da ka iya kawo tarnaƙi ga ci gaban masaratun ko kuma kawar da su, wanda suka ce yin akasin hakan ba zai haifar da ɗa mai ido ba, kuma na iya kawo ruɗani da koma baya tare da rashin tabbas na samun ci gaban tsaro da kwanciyar hankali a jihar.

Ka karanta wanna: Ƴar Tik Tok Ta Yi Ɓatan Dabo: Al’ummar Kano Na Ce-Ce-Kuce Kan Sharuɗɗan Beli

Don haka, takardar koken ta bukaci majalisar dokokin ta jiha da ta yi watsi da masu neman waccar bukatar, (COPDORG) kuma sun ce “tun daga buƙatar ta farko da waccar ƙungiya ta miƙa ya kamata a yi watsi da su, domin roƙon nasu ba shi da wata fa’ida ga ci gaban jama’ar jihar Kano”, in ji su.

Suna ƙara ba wa shugaban majalisa da ‘yan majalisa baki ɗaya da kuma ɓangaren zartarwa wato Gwamnati shawarar ya kamata su tsaya tsayin daka domin yin abubuwan da suka dace da zaman lafiya da bunƙasar rayuwar jama’a, jihar Kano, musamman a wannan mawuyaci hali, wanda al’umma ke fama da matsanaciyar wahalar rayuwa. Kuma su guji duk abin da ka iya rura wutar rikici da taɓa mutuncin ‘yan kasa masu bin doka da oda na jihar Kano.

Ka karanta wanna: Ko Ka San Burushin Wanke Haƙora Na Iya Tasiri Ga Lafiyar Baki Da Jikin Dan Adam?

“Muna so mu tabbatar wa majalisa cewa, mutane suna son Sarakunansu da masarautarsu; a kauce ɗaukar duk wani mummunan mataki ko soke tsarin gudanarwar tsarin masarautu a yanzu haƙiƙa zai lalata zaman lafiya da tsaro wanda zai iya haifar da rashin jituwa gaba ɗaya.

Ƙungiyar ta ƙara kira ga mai girma shugaban majalisa ya kamata a yi watsi da wadancan soki-burutsun maganganu marasa daɗin ji don kauce wa ruɗani da rikici a jiharmu abar ƙaunarmu, kuma ta haka ne za a kauce wa yanayin da za a iya kallon mu a matsayin abin dariya, ko ma’abota rashin son ci gaba ƙasa da kuma haifar da tashin hankali .”

← Back

Thank you for your response. ✨

1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Majalisar Dokokin Jahar Kano Za Ta Gyara Dokar Ƙarin Shekaru 5 Na Aikin Gwamnati - The StentorNews Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...