Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Shaharrariyar Ƴar Tiktok Murja Kunya Ta Faɗa Komar Hisbah A Kano

Kunya
Kunya

Daga Wakilinmu

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama Murja Ibrahim Kunya, fitacciyar ƴar Tiktok da ta yi suna a shafukan sada zumunta na zamani bisa zargin yaɗa baɗala.

A safiyar ranar Talata ne wani gidan rediyo a Kano da wasu daga shafukan sada zumunta suka yaɗa rahoton kama Murja Kunya.

Hukumar Hisbah ta nemi damke akalla mashahuran ’yan Tiktok su shida da ake zargi da yada bidiyoyin Baɗala ciki har da Murja, a shafukansu na Tiktok da sauran kafafen sada zumunta na zamani matakin da hukumar ta ce ya saɓa wa dokokinta.

Idan za’a iya tunawa ko a baya-bayan nan babban kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya gayyaci ɗaukacin mata ‘yan Tikto da ke Kano zuwa wani zama inda hukumar ta yi tayin gyara musu sana’o’i su da kuma basu tallafin karatu domin kyautata rayuwar su.

Bayan waccar gayyata ne sai Murja da sauran abokanta da ake nema ruwa a Jallo suka fitar da wani Bidiyon da Hisbar ta ce ya saɓawa koyarwar Addinin musulunci da kuma al’adar Malam Bahaushe.

Kafar yaɗa labarai ta STENTORNEW ta tuntuɓi mai magana da yawun hukumar hisbah, Malam Lawan Ibrahim Fagge wanda ya tabbatarwa da wakilinmu kamun na Murja a daran jiya litinin.

Lawan fagge ya ce ” Dakarunmu na hisbah sun kama ta da misalin ƙarfe 11 na dare, bayyan saurayinta ya maido ta gida a unguwar Tinshama.
” Ya ce kamun ya na da nasaba da ƙorafi da muka samu daga maƙoftanta baya ga kaucewa yarjejeniyar da mukai da ita da kuma sauran abokan yaɗa baɗalar, kuma zarar mun kammala bincike za mu gurfanar da ita gaban ƙuɗiya domin ta girbi abin da ta shuka”. Inji kakakin hisbah.

2 Comments

2 Comments

  1. Pingback: Ƴar Tik Tok Ta Yi Ɓatan Dabo: Al'ummar Kano Na Ce-Ce-Kuce Kan Sharuɗɗan Beli - The StentorNews Hausa

  2. Pingback: Shugaban Kanfanin TikTok Ya Gargaɗi Amurka Kan Haramta Shafin - The StentorNews Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...