Mu’azu Harɗawa daga Bauchi
Hukumar zaɓe mai zaman kanta a jihar Bauchi ta tabbatar da zaɓen da aka gudanar a mazaɓu hudu na majalisar dokokin jihar a matsayin wanda ya samu gagarumar nasara da zaman lafiya a faɗin rumfunan zabe 42 a jihar.
Read also: Gwamnan Bauchi Bala Mohammed Ya Ƙaddamar da Hasken Solar a Dajin Yankari
Read also: Matashi Mai Shekara 24 Ya Kashe Mahaifinsa A Bauchi
Alhaji Mohammed Nura, shi ne kwamishinan zaɓe na INEC mai zaman kanta, ya tabbatar da hakan bayan ya sa ido kan wasu rumfunan zaɓe a Bauchi a ranar Asabar. Ya ce basu sami ƙorafin rashin wadattatun kayan aiki ba ko kuma tangarɗar na’urorin zaɓe, kayan aiki, ko kuma ɓacewar sunayen masu kaɗa ƙuri’a da sauran su ba..
Read also: Za a Fara Jigilar Alhazan Jihar Bauchi Daga Ranar 7 Ga Watan Mayu
Nura ya bayyana cewa an gudanar da zaɓen ne a rumfunan zaɓe 42, inda ya ƙunshi mazaɓun ƴan majalisar jiha huɗu a kananan hukumomi uku, na Bauchi, Ningi, da Katagum. Ya yaba wa masu kada ƙuri’a kan yadda suke gudanar da zaɓe cikin ɗa’a da kuma fitowar jama’a masu yawa, inda ya nuna gamsuwa da kishin da suke da shi na jefa ƙuri’unsu cikin lumana.
Ya ce hakan ya ba shi ƙwarin gwiwa daga ɗimbin masu kaɗa ƙuri’a, Nura ya sanar da hukumomin tsaro da su tura ƙarin ma’aikata don kula da jama’a. Ya jaddada muhimmancin jam’iyyun siyasa masu bin ƙa’ida, da karya lagon masu ƙwace ƙuri’u, da sayen ƙuri’u, da kuma yin ƙarya. Hukumar ta INEC ta kuma gargadi masu kada ƙuri’a da su kaucewa yin katsalandan a lokacin ƙidaya da kuma yayin sanar da sakamakon zaɓe, inda ya bukace su da su kiyaye da bada tazarar mita 10-15 daga cibiyar bayan kada ƙuri’a su.




























