Daga Abdu Ado
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya raba wa masu bukata ta musamman tallafin naira dubu ashirin (N20,000) kowannen su.
Read also: Gwamnatin Kano Ta Sanar da Hutun Bikin Takutaha
Da yake bayar da tallafin a dakin taro na gidan gwamnati, Gwamna Abba Yusuf ya ce gwamnatin sa ta yake shawarar bayar da tallafi ne domin taimaka wa masu larura ta musamman domin saukaka musu matsanacin halin rayuwa da ake ciki.
Gwamna ya ce masu bukata ta musamman na sawun gaba a gwamnatin sa don haka baza su zama daban ba wajen taimakawa rayuwarsu a wannan gwmantin.
” Ba zan manta da gudunmawar da kuka bamu ba a lokacin yakin neman zabe don haka za mu ci gaba da kula da walwalar ku ba tare da nuna banbancin domin halin da ku ke ciki ba” inji gwamna.
Ya kuma ba su tabbacin samar da hukuma wadda zata dinga kula da masu bukata ta musamman a gwamnatin sa nan bada jumawa ba, tare da kira gare su da su yi amfani da tallafin da suka samu ta hanyar da ta dace domin bunkasar rayuwarsu.
Kimanin masu bukata ta musamman guda dubu biyu (2000) da ga Kanana Hukumomi 44 na jihar kano suka ci gajiyar shirin.
Read also: Gwamnatin Kano Ta Naɗa Sheikh Bazzallah Nasir Kabara A Matsayin Shugaban Hukumar Tace Fina-finai
Wadanda suka sami tallafin sun hadar da Makafi da Guragu da Zabiya da kurame da kuma masu larurar yatsu da na laka.
A jawabinsa Shugaban masu bukata ta musamman na jihar Kano, Engr. Musa Muhammad Shaga, ya gode wa gwamna bisa cika alkawarin sa na tallafawa masu bukata ta musamman tun lokacin yakin neman zabe




























