Connect with us

Hi, what are you looking for?

Tsaro

Rundunar Yan Sanda Sun Bankado Shirin Kona Gidan Gwamnatin Jihar Kano

Kano CP
Kano CP

Rundunar ‘yan sanda jihar Kano, ta ce ta bankado wani shiri da wasu marasa kishin kasa ke yunkurin yi na kona gidan gwamnatin jihar Kano a kan shari’ar da ake ci gaba da yi a kotun koli kan zaben gwamna tsakanin jam’iyyar NNPP da APC.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Muhammad Usaini Gumel ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a wani taro da shugabannin kafafen yada labarai, gabanin zaman kotun koli na daukaka kara kan shari’ar kujerar gwamnan Kano da aka shirya gudanarwa yau Alhamis 21 ga watan Disamba, a Abuja.

Gumel ya bukaci kwararrun kafafen yada labarai da su sanar da jama’a yadda ya kamata a kan abubuwan da ke faruwa bisa tsari da gaskiyar labari.

A cewarsa bai kamata a samu tashin hankali a Kano ba domin maganar tana kotun koli da ke Abuja ba a jihar ba.
Haka zalika Kwamishina ya ce rundunar a shirye take ta murkushe duk wani mutum ko gungun muta ne da za su yi yunkurin tayar da zaune tsaye a jihar ta Kano.
Ya kuma ja hankalin jama’a da su sanar da hukumar a bisa duk wani labarin da suka samu wanda ba su yadda da shi ba cikin hanzari ga humar ko ofishin ‘yan sanda mafi kus.
(Solacebase)

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...